Ana Fargabar Yaki bayan Amurka Ta Tabo Rasha, Gwamnatin Putin Ta Magantu

Ana Fargabar Yaki bayan Amurka Ta Tabo Rasha, Gwamnatin Putin Ta Magantu

  • Rundunar sojin Amurka ta kwace jirgin dakon mai da ya ke dauke da tutar Rasha da ke da alaƙa da Venezuela bayan bin diddigi na mako biyu
  • Gwamnatin Rasha ta soki matakin, tana mai cewa an karya dokokin kasa da kasa kan yadda ake tafiyar da jiragen ruwa a cikin tekuna
  • Hakan ya zo ne a cikin wani yunƙurin Amurka wajen aiwatar da takunkumin da ta sanya wa jigilar mai daga Venezuela zuwa wasu kasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa ta kwace tankar mai dauke da tutar Rasha mai suna Marinera — wanda a da aka sani da Bella-1 — a tsakiyar Tekun Atlantika.

Hakan ya faru ne bayan bin diddigi na mako biyu da rundunar sojin ruwan Amurka ke yi, a matsayin wani mataki na tilasta takunkumin Amurka a kan kasar Venezuela.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da Ganduje suka fadawa Abba ana batun shigarsa APC

Shugabannin kasashen Amurka da Rasha
Shugaban Amurka da Rasha suna jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin Washington da Moscow yayin da kasashen Turai da wasu abokan hulɗa ke lura da tasirin wannan mataki.

Amurka ta kwace jirgin kasar Rasha

Rundunar sojin Amurka ta ce an kama jirgin Rasha ne bisa umarnin wata kotun kasar saboda karya takunkumin da aka sanya wa jigilar man fetur daga Venezuela.

Jirgin, wanda a da ake zargin yana ɗauke da mai wanda aka haramta wa jigila, ya tsere daga kokarin hukumar kiyaye ruwan Amurka na tona masa asiri yayin da yake kokarin shiga ko fita daga ruwa kusa da Venezuela.

An ce a kan hanyarsa ne a cikin Tekun Atlantika ya canza suna zuwa Marinera kuma aka sa tutar Rasha domin bayyana cewa yana cikin ikon ƙasar, amma Amurka ta ce hakan ba zai hana aiwatar da takunkumin da aka sanya masa ba.

Martanin kasar Rasha ga Amurka

A cikin martanin ta, Ma’aikatar Sufurin Rasha ta soki wannan mataki na Amurka, tana mai cewa ya saba wa Dokar Tekun Duniya na 1982 wadda ta tanadi ‘yancin zirga-zirga cikin lumana a ruwan duniya.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba Abubakar Malami, matarsa da dansa beli, za su biya N1.5bn

Ma’aikatar ta kara da cewa an haɗa jirgin ne bisa ka’ida a ƙarƙashin tutar Rasha daga ranar 24, Disamba, 2025, kuma tura jirgin da karfi a cikin teku ba tare da izinin wata ƙasa ba ba daidai ba ne.

Rahoton Sky News ya nuna cewa Rasha ta yi kira ga Amurka da ta tabbatar da kula da mutuncin da ‘yancin ma’aikatan jirgin – musamman mazauna Rasha da ke cikinsa – sannan su maido da su gida cikin gaggawa.

Wasu masu sharhi na cewa duk da ba a samu rikici tsakanin sojojin Amurka da Rasha kai tsaye ba, matakin na iya tayar da rikici a manyan kasashen duniya wanda zai iya kaiwa ga yaki ko da ta bayan fage ne.

Jirgin ruwa na tafiya a teku
Wani jirgin ruwan daukar kaya na tafiya a cikin teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump zai karbi iko da Greenland

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta ce tana cigaba da duba batun karbar babban tsibirin Greenland da ke kasar Denmark.

Sanarwar da fadar White House ta fitar ta nuna cewa Amurka za ta iya amfani da karfin soja idan ta kama domin karbar tsibirin.

Biyo bayan sanarwar, shugabannin kasashen Turai da suka hada da Faransa, Spain, Italy da sauransu sun ce ba za su yarda da matakin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng