Yadda Burkina Faso Ta Daƙile Shirin Kashe Shugabanta Traore

Yadda Burkina Faso Ta Daƙile Shirin Kashe Shugabanta Traore

  • Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki da aka shirya kashe Shugaba Ibrahim Traoré
  • An zargi tsohon jagoran mulkin soji, Laftanar Kanar Paul Henri Damiba, da jagorantar shirin daga ƙasashen waje
  • Ministan tsaro na kasar ya ce an samu hujjoji da dama ciki har da bidiyo da kuma tallafin kuɗi daga Ivory Coast

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Burkina Faso - Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso ta sanar da cewa ta dakile wani sabon shirin juyin mulki da aka tsara domin kashe shugaban ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré.

Ministan tsaron ƙasar, Mahamadou Sana, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi da daddare a gidan talabijin na ƙasa.

Ibrahim Traore ya tsallake rijiya da baya
Shugaban mulkin Sojan Burkina Fasa, Ibrahim Taore yayin girmama sojojin kasar Hoto: Wwe Love President Ibrahim Traore
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa a cewar sanarwar, ana zargin tsohon jagoran mulkin soji, Laftanar Kanar Paul Henri Damiba, da kitsa harin.

Kara karanta wannan

Bayan hango jirgin Amurka a Abuja, Trump na iya kai farmaki Greenland

An dakile shirin kashe Shugaban Burkina Faso

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Damiba dai shi ne jami’in soja da Traoré ya kifar da mulkinsa a watan Satumban 2022.

An kama masu shirin kifar da gwamnatin Ibrahim Traore
Shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore Hoto: Born Gay
Source: Getty Images

A kuma cewar Ministan Burkina Faso:

“Hukumomin leƙen asirinmu sun gano wannan shiri a kurarren lokaci. Sun yi niyyar kashe Shugaban Kasa, sannan su kai hari kan wasu manyan cibiyoyi da fitattun fararen hula.”

Ya ƙara da zargin cewa an samu kuɗin aiwatar da shirin ne daga makwabciyar kasa, Ivory Coast, zargin da har yanzu ba a ce komai a kansa ba.

Burkina Faso ta bankado shirin juyin mulki

Mahamadou Sana ya ce an gano wani bidiyo da ya fallasa masu shirin suna tattauna yadda za su kashe shugaban ƙasa, ko dai ta hanyar harbi kai tsaye ko dasa bama-bamai a gidansa.

A cewarsa, an shirya kai harin ne da misalin 11.00 na dare a ranar Asabar, 3 ga Janairu, inda ake sa ran kashe Shugaban Kasan.

Kara karanta wannan

Kwanaki bayan munanan hare hare a Neja, manoma sun ci karo da bam a gona

Bayan haka, an ce masu shirin za su kai hare-hare kan manyan jami’an soja da fararen hula domin kammala aikinsu.

Sana ya yi zargin cewa Damiba ya tara sojoji da fararen hula masu goyon bayansa, ya kuma samu tallafin kuɗi daga waje.

Ministan ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike tare da cafke mutane da dama, yana mai cewa za a gurfanar da su gaban shari’a nan ba da jimawa ba.

Tun bayan karɓar mulki, Kyaftin Traoré ya fuskanci aƙalla yunkurin juyin mulki biyu, tare da ƙalubalen hare-haren ‘yan ta’adda da suka tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Burkina Faso ta saki jami’an sojin saman Najeriya 11 da ta tsare tsawon kwanaki tara, biyo bayan tattaunawar diflomasiyya.

Sakin jami’an ya zo ne jim kaɗan bayan kammala ziyarar wata tawagar diflomasiyya daga Najeriya zuwa birnin Ouagadougou, inda aka gudanar da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati.

Masu sa ido kan harkokin tsaro a yankin sun bayyana lamarin a matsayin babbar nasara ta diflomasiyya, wacce ta kawo ƙarshen wani lamari da ya tayar da hankula a Yammacin Afrika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng