Bayan Hango Jirgin Amurka a Abuja, Trump na Iya kai Farmaki Greenland
- Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa amfani da sojojin ƙasa wajen karbe Greenland na iya zama zaɓi cikin manufofin ta, abin da ya jawo suka daga kasashen Turai
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce sarrafa Greenland na da muhimmanci saboda tsaro, inda ya ce akwai ƙoƙarin hana China da Rasha su ƙara tasiri a yankin
- Jagororin ƙasashen Turai da na Denmark sun jaddada cewa Greenland “na mutanen sa ne” kuma shawarar siyasa game da makomar garin ya rataya ne a hannun Denmark
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Gwamnatin Amurka ta jefa sabuwar muhawara ta diflomasiyya yayin da take nuna cewa amfani da rundunar sojojin ƙasar na iya kasancewa wani zaɓi domin samun ikon tsibirin Greenland, wanda ke ƙarƙashin mulkin ƙasar Denmark.
Wannan lamari ya jawo martanin ƙasashen Turai da Canada, waɗanda suka yi tir da ra’ayin da suka ce zai saba ƙa’idojin kasa da kasa da girmama ikon Greenland.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ce hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara yin taka-tsantsan kan batutuwan tsaro a yankin Arctic, inda ake ganin Greenland na da matuƙar mahimmanci saboda matsayinsa a tsakiyar Turai da Arewacin Amurka.
Kasar Amurka na son karbe Greenland
Amurka ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Donald Trump, yana ganin samun iko kan Greenland wata babbar manufa ce ta tsare-tsaren kasashen waje, musamman domin kawo cikas ga abokan gaba a yankin Arctic.
Fadar White House ta ce akwai tattaunawa kan hanyoyi daban-daban da za a bi wajen cimma wannan buri, kuma amfani da sojojin Amurka yana daga cikin zaɓuɓɓukan da shugaban ƙasa zai iya dubawa idan ya zama dole.
Sai dai wasu jami’an Amurka ciki har da shugaban Majalisar Wakilai, Mike Johnson, sun nuna rashin goyon bayan su ga amfani da soji a Greenland, suna mai cewa hakan bai dace ba.
Martanin Turai da Canada ga Amurka
Rahoton Reuters ya ce kasashen Turai da dama sun yi tir da zancen Amurka na neman mamaye yankin Greenland da shugaba Donald Trump ke son yi.
Shugabannin Faransa, Burtaniya, Jamus, Italiya, Poland, Spain da Denmark sun fitar da sanarwa tare da jaddada cewa Greenland “na mutanen sa ne”, kuma makomar tsibirin na ƙarƙashin ikon Denmark da Greenland ne kadai.
Shugabar gwamnatin Denmark, Mette Frederiksen, ta ƙara jaddada cewa Greenland ba na kasuwanci bane ko sayarwa ga wata ƙasa.

Source: Getty Images
Haka nan Firaministan Canada, Mark Carney, ya bayyana goyon bayan kasar sa ga Denmark da mutanen Greenland wajen yanke shawarar makomar yankin.
Greenland ne tsibirin da ya fi girma a duniya, kuma yana da muhimmanci sosai wajen harkokin tsaro, musamman wajen kula da hanyoyin jiragen ruwa da sararin samaniya a yankin Arctic.
Jirgin Amurka ya sauka a Abujan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa an hango wani jirgin sojojin Amurka mai jigilar kayayyaki ya sauka a filin jirgin kasa da kasa da ke Abuja.
Lamarin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan sojojin Amurka sun kawo hari Arewa maso Yammacin Najeriya a shirin yaki da ta'addanci.
Wani mai sharhi kan tsaro a nahiyar Afrika, Brant Philip ya bayyana cewa jirgin ya sauka ne a Abuja bayan tasowa daga kasar Senegal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

