Jerin Kasashe 3 da Amurka Ta Kutsa da Karfi Ta Kama Shugabanninsu
Kama shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, da Amurka ta yi da karfin soja ya sake tayar da muhara a kan kasashen duniya da kasar ta kutsa da kama shugabanninsu a tarihi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa sun kama shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro.
Tarihi ya nuna cewa ba Maduro ba ne shugaban kasa na farko da Amurka ta shiga har kasarsa ta kama shi tare da yanke masa hukunci.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun yi dubi zuwa ga tarihi mun tattaro muku jerin shugabannin duniya da Amurka ta shiga kasarsu ta kama su suna kan mulki.
1. Amurka ta kama shugaban Panama a 1989
A watan Disamba na shekarar 1989, Amurka ta ƙaddamar da mafi girman farmaki tun bayan Yaƙin Vietnam — wato mamayar ƙasar Panama domin kawar da shugaban mulkin soja na kasar, Manuel Noriega.
Washington ta zarge shi da cin hanci da rashawa, maguɗin zaɓe, da safarar miyagun ƙwayoyi, irin zarge-zargen da take yi wa Maduro bayan shekaru 36.
Rahoton US Today ya nuna cewa Noriega, wanda a da ya kasance abokin Amurka, an kama shi, aka kai shi Miami, inda aka gurfanar da shi bisa zargin safarar ƙwaya.

Source: Getty Images
Bayan ya yi zaman gidan yari a Amurka da Faransa, daga bisani an mika shi ga Panama, inda ya rasu a gidan yari a shekarar 2017.
2. Amurka ta kama shugaban Iraq, Saddam
An kama shugaban kasar Iraq, Saddam Hussein ne a ranar 13, Disamba, 2003, watanni tara bayan fara mamayar da Amurka da kawayenta suka jagoranta.
An farmaki Saddam ne bisa bayanan leƙen asiri na ƙarya da suka yi ikirarin cewa Bagadaza na da makaman kare dangi (WMD).
Al-Jazeera ta wallafa cewa kamar Manuel Noriega, Saddam ya kasance abokin hulɗa na Amurka na tsawon shekaru, musamman a lokacin yaƙin Iraq da Iran a shekarun 1980, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan 1.
Haka kuma, kafin yaƙin 2003, Amurka ta yi ikirari ba tare da hujja ba cewa Saddam na tallafa wa ƙungiyoyin ’yan bindiga irin su al-Qaeda.

Source: Getty Images
Sai dai daga bisani, ba a taɓa gano ko a samu makaman kare dangi a ƙasar ba, kuma an gano Saddam yana ɓoye ne a cikin wani rami kusa da garinsa na Tikrit.
An gurfanar da shi a gaban kotun Iraki, inda aka yanke masa hukuncin kisa, wanda daga bisani aka aiwatar ta hanyar rataya saboda laifuffukan cin zarafin bil’adama a ranar 30, Disamba, 2006.
3. Amurka ta kama shugaban Venezuela
A Janairun 2026, shugaba Donald Trump ya sanar da cewa Amurka ta kama shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, tare da matarsa Cilia Flores, bayan abin da ya bayyana a matsayin “babban farmaki” zuwa kasar.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin ayyukan jiragen sama da na ruwa na Amurka a faɗin Tekun Caribbean da gabashin Tekun Pacific.
Amurka ta kama shugaban kasar Venezuela bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, yayin da wasu ke cewa mamayar tattalin arziki ce ta sanya Trump ya kai farmaki kasar.

Kara karanta wannan
Bayan yiwa shugaba Maduro daukar amarya, Amurka za ta kwashe man fetur a Venezuela

Source: Getty Images
BBC ta rahoto cewa Washington ta fitar da hotunan Maduro sanye da ankwa a hannaye yayin isowarsa birnin New York, yayin da gwamnatin Trump ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotun Amurka.
Amurka ta kawo hari Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa sojojinsa sun kawo farmaki Arewa maso Yammacin Najeriya.
A bayanin da Trump ya yi, ya ce sun kawo harin ne kan 'yan ta'addan ISWAP a yankin, duk da wasu rahotanni sun ce babu tarihin 'yan ISWAP a Sokoto.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa da sanin ta aka kai harin, tare da karin bayani da cewa ita ta bayar da bayanan sirri ga Amurka.
Asali: Legit.ng

