Jerin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda 8 da Amurka Ta Fi Damuwa da Ayyukansu a Najeriya da Afirka
A makon da ya gabata ne Amurka ta kawo farmaki jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya da nufin kakkabe 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar ISIS.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da kai wadannan hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin masu karfi da kuma hadari ga ‘yan ta’adda.

Source: Getty Images
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Ma'aikatar yaƙi ta Amurka ta fitar, sannan ta wallafa a shafinta na X a daren Juma'a.
Harin Amurka ya ja hankali a Najeriya
Wannan farmaki ya ja hankalin mutane a ciki da wajen Najeriya, inda wasu ke ganin hakan gazawa ce ga gwamnati mai ci, wasu kuma na ganin matakin zai iya taka rawa a yaki da ta'adda.
Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta tabbatar da kai hare-haren, tana mai cewa an yi ingantattun shirye-shirye da musayar bayanan sirri kafin kai farmakin.
Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta sanya Najeriya a jerin kasashen da ake da damuwa kan yancin addini saboda zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi.
Jerin kungiyoyin da Amurka ta damu da su
A wata sanarwa da gwamnatin Amurka ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta jero wasu kungiyoyin 'yan ta'addda a Najeriya da Afirka da ta sanya su a jerin kungiyoyi masu hadari.
A wannan rahoton, mun tattaro muku kungiyoyin 'yan ta'adda takwas da Amurka ta fi damuwa da ayyukansu na ta'addanci a Najeriya a wasu sassan nahiyar Afirka.
1. Kungiyar Boko Haram
Boko Haram, wadda a hukumance ake kira Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad (JAS), an kafa ta ne a shekarar 2002 ta hannun Mohammed Yusuf.
Kungiyar ta fara daukar makamin tare da tayar da bore a watan Yuli na 2009 da nufin kifar da gwamnatin Najeriya tare da kafa ƙasa bisa tsauraran fassarar dokokin Musulunci, in ji rahoton PR Nigeria.
Duk da gwamnatin tarayya na ikirarin nakasa ta, kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci da suka zama barazana ga tsaron Najeriya.
2. Kungiyar ISWAP
Kungiyar ISIS ta Yammacin Afirka, wadda aka fi sani da Islamic State West Africa Province (ISWAP), na ɗaya daga cikin rassan ISIS mafi muhimmanci ta fuskar ta'addanci a duniya.
Ƙungiyar ta balle daga Boko Haram a shekarar 2016 kuma ta ci gaba da kai hare-hare a Najeriya da yankin Tafkin Chadi, kamar yadda BBC News ta tattaro.

Source: Facebook
Zuwa ƙarshen 2025, ISWAP ta zama babbar barazana a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, yayin da wasu sababbin ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS suka fara bulla a Arewa maso Yamma.
3. Kungiyar ADF
Kungiyar ta'addanci ta ISIS–DRC wacce ta fi shahara da sunan Allied Democratic Forces (ADF) a Afirka ta Tsakiya na cikin kungiyoyin da suka tsayawa Amurka a wuya.
Ƙungiyar ta fi gudanar da ayyukanta a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da kuma ƙasar Uganda da ke makwabtaka da kasar.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
An ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci ta kasa da ƙasa saboda hare-haren tashin hankali da take kaiwa a yankin, kamar yadda jaridar VOA ta kawo.
4. Kungiyar ISMP a Mozambique
Kungiyar ta'addanci ta ISMP, wacce ke da alaka da ISIS tana kai hare-hare kan fararen hula a lardin Cabo Delgado da ke Arewacin ƙasar Mozambique.
A rahoton da cibiyar yaki da ta'addanci (NCTC) ta wallafa a yanar gizo, kungiyar na da burin kifar da gwamnatin Mozambique tare da kafa tsarin mulki bisa tsauraran dokokin Shari’a.
5. Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM)
Kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) kungiya ce ta 'yan ta'adda da ke Mali kuma tana aiki a yawancin kasashen Yammacin Afirka, ciki har da sassan Burkina Faso da Nijar.
Ƙungiyar JNIM, wadda ke da alaƙa da al-Qaeda, ta fara faɗaɗa ayyukanta na kai hare-hare zuwa Najeriya, kamar yadda rahoton Al-Jazeera ya tabbatar.
Ƙungiyar ta ɗauki alhakin kai hare-hare da dama, lamarin da ya nuna yadda ta faɗaɗa ayyukanta fiye da inda take da sansani a yankin Sahel.
6. Kungiyar ISIS ta yankin Sahara (ISIS-GS)
Kungiyar IS ta yankin Sahara watau ISIS-GS na cikin kungiyoyin 'yan ta'adda da Amurka ke ganin suna da hadari a nahiyar Afirka.
Kungiyar da ake kira da ISSP a takaice, na gudanar da ayyukanta a yankin Liptako-Gourma, wanda wannan yankin ya hada iyaka da ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar.
Ana ganin wannan yanki ya kasance cibiyar ayyukan 'yan tawaye, kuma ƙungiyar ta kasance wani reshe na ISIS, kamar yadda Jaridar Sunatimes ta rahoto.
7. Kungiyar ISLP ta Libya
Kamar dai sauran, wannan kungiyar 'yan ta'adda ta ISLP reshe ne na ISIS, wacce ta bayyana bayan tawayen 2011 a kasar Libya.
Jaridar The Washington ta ce tun daga wannan lokacin, kungiyar take kai kai hare-hare tare kan fararen hula da jami'an tsaro tare da kwace yankuna a kasar Libya.
Ta yi amfani da rikicin siyasa wajen kafa rassanta a Cyrenaica, Tripolitania da Fezzan, sannan ta kwace birane kamar Derna da Sirte, tare da kai munanan hare-hare, ciki har da kisan Kiristocin Coptic a 2015.
Duk da cewa an raunana ƙungiyar sosai sakamakon matakan da sojojin Libya da Amurka suka dauka, rahotanni sun nuna cewa ragowarta na ci gaba da aiki a cikin yanayin rashin tsaro.
8. Ansar al-Shari’a a Tunisia
Rahoton NCTC ya nuna cewa an kafa kungiyar Ansar al-Shari’a a Tunisia (AAS-T) a shekarar 2011, kuma ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi masu da'awar jihadi a ƙasar.
Daga baya an ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci a matakin ƙasa da ƙasa, sannan kuma gwamnatin Tunisia tasanya ta a jerin haramtattun kungiyoyi.
Duk da cewa ayyukan kungiyar sun ragu sosai sakamakon matakan tsaro, wasu rahotanni sun nuna cewa ragowar ‘ya’yanta na iya ci gaba da aiki a ɓoye ko kuma sun sauya suna.

Source: Twitter
Ƙasar Amurka ta ayyana waɗannan ƙungiyoyi a matsayin manyan barazana saboda munanan ayyukansu da tasirin da suke da shi wajen tayar da hankula a Najeriya da sauran sassan Afirka.
Nasarar harin Amurka a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta fara bayanin nasarar da aka samu kan yan ta'adda a farmakin da Amurka ta kai jihar Sakkwato.
DHQ ta bayyana harin da Amurka ta kawo a matsayin wanda aka yi bisa sahihan bayanan sirri kuma mai matuƙar tasiri.
Haka kuma, ta gargadi al’umma da su guji ɓoye ko taimaka wa ’yan ta’addan da ke tserewa bayan sun ji ruwan bama-bamai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




