Hana Biza: Mali, Burkina Faso Sun Rama Abin da Trump Ya Musu kan 'Yan Amurka
- Kasashen Mali da Burkina Faso sun sanar da daukar matakin ramuwar gayya kan takunkumin tafiye-tafiye da Amurka ta kakaba musu
- Matakin ya zo ne bayan shugaba Donald Trump ya saka kasashen cikin jerin wadanda aka takaita shigarsu Amurka a kwanakin da suka wuce
- Rahotanni sun nuna cewa hukumomin kasashen biyu sun ce abin da suke yi ya ta’allaka ne kan ka’idar daidaito da mutunta ikon kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Burkina Faso – Gwamnatocin kasashen Mali da Burkina Faso sun bayyana shirinsu na kakaba takunkumin biza ga ‘yan kasar Amurka.
Sun yi haka ne a matsayin martani ga sabon matakin da gwamnatin Amurka karkashin shugaba Donald Trump ta dauka na hana ‘yan kasashen biyu shiga cikinta.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan Trump ya fadada jerin kasashen da aka hana ko takaita shigarsu Amurka, inda aka saka Mali da Burkina Faso cikin jerin.
Martanin Mali kan matakin Amurka
Ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa-da-kasa ta Mali ta bayyana cewa duk wani dan Amurka da ke shirin shiga kasar zai fuskanci sharudda da ka’idojin daidai da wadanda hukumomin Amurka ke daurawa ‘yan Mali masu neman shiga Amurka.
A cewar ma’aikatar, an dauki wannan mataki ne “a matsayin ka’idar ramuwar gayya kuma zai fara aiki nan take.” Ta kara da cewa Mali na da hakkin kare martabarta da ‘yancin ‘yan kasarta a duk wata mu’amala ta kasa-da-kasa.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Mali ke kara nisantar kasashen Yamma, tare da mayar da hankali kan sababbin tsare-tsaren tsaro da hadin gwiwa da wasu kasashe.
Matakin Burkina Faso kan Amurka
A nata bangaren, Burkina Faso ta bayyana cewa ita ma za ta kakaba matakan hana biza ga ga ‘yan kasar Amurka kamar yadda Trump ya mata.
The Guardian ta rahoto cewa gwamnatin kasar ta jaddada cewa duk da wannan mataki, tana nan daram kan mutunta juna da kuma bin ka’idar ramuwar gayya a huldar kasa-da-kasa.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
Hukumomin kasar sun bayyana cewa ba su dauki matakin ne don tayar da rikici ba, sai dai domin nuna cewa Burkina Faso ba za ta amince da duk wani mataki da zai wulakanta ‘yan kasarta ba tare da martani ba.
Mali da Burkina Faso, tare da Nijar, na daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar AES, inda suke kokarin rage dogaro da kasashen Yamma.

Source: Twitter
Dukkan kasashen ukun na karkashin shugabannin soji, kuma sun kara kusantar Rasha, tare da korar sojojin Faransa da Amurka daga kasashensu.
Amurka ta kai hari kasar Venezuela
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya sanar da cewa ya kai wani hari kasar Venezuela.
A bayanin da ya yi, Trump ya sanar da 'yan jarida cewa ya kai harin ne a wani waje da ake loda kaya a jirgin ruwa kuma ya yi barna sosai.
Trump bai bayyana hakinanin wajen da ya kai harin ba, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoton kasar Venezuela bata yi martani ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
