Sojan da Ya Yi Juyin Mulki Ya Zama Zababben Shugaban Kasar Guinea
- Shugaban juyin-mulkin Guinea, Mamady Doumbouya, ya lashe zaben shugaban kasa na farko tun bayan karbe iko da sojoji suka yi a 2021
- Sakamakon wucin-gadi ya nuna Doumbouya, ya samu kaso mafi rinjaye na kuri’u, lamarin da ya ba shi damar kaucewa zagaye na biyu a zaben
- Zaben ya zo ne a daidai lokacin da masu saka ido ke ce-ce-ku-ce kan sahihancinsa da kuma makomar dimokuradiyya a kasar Guinea
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Guinea – Shugaban juyin-mulkin Guinea, Mamady Doumbouya, ya lashe zaben shugaban kasa bisa sakamakon wucin-gadi da aka sanar bayan kammala kada kuri’a.
Wannan ne karo na farko da aka gudanar da zabe a kasar tun bayan juyin-mulkin soji da ya kifar da gwamnatin farar hula a 2021.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa sakamakon da hukumar zabe ta sanar ya nuna Doumbouya ya samu kaso 86.72 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar 28, Disamba, 2025.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
Sakamakon zabe da dokar kasar Guinea
Hukumar zabe ta kasar Guinea ta ce alkaluman da aka fitar sakamakon wucin-gadi ne, kuma Kotun Koli na da kwanaki takwas domin tantancewa da tabbatar da sakamakon, musamman idan aka samu kalubale daga bangarorin da ke da korafi.
Rahotanni sun nuna cewa kaso 80.95 cikin 100 na masu rijistar zabe kimanin miliyan 6.7 ne suka fito suka kada kuri’a, abin da hukumomi ke kallon a matsayin nuna sha’awar jama’a ga tsarin sauyin mulki zuwa farar hula.
Duk da haka, BBC ta rahoto cewa masu sukar zaben na cewa yanayin siyasar kasar bai ba da cikakkiyar dama ga 'yan adawa domin fafatawa ba.
Juyin-mulki da sojoji su ka yi a Guinea
Mamady Doumbouya ya karbe iko ne a 2021 bayan hambarar da shugaba Alpha Conde, wanda ya shafe shekaru yana mulki a kasar tun daga 2010.
Bayan juyin-mulkin, Doumbouya ya yi alkawarin cewa shi da sauran jami’an soja ba za su tsaya takarar dukkan zaben da za a yi ba.
Sai dai daga bisani, kuri’ar raba gardama da aka gudanar ta sauya wannan tsari, inda aka ba jami’an soja damar tsayawa takara tare da tsawaita wa’adin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai.

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa wannan sauyi ya bude kofar tsayawar Doumbouya takara, matakin da ya jawo suka daga bangarori daban-daban a kasar.
Paul Biya ya lashe zaben Kamaru
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Kamaru da ya shafe shekaru da dama yana kan mulki ya sake lashe zaben da aka yi.
Paul Biya ya samu mafi rinjayen kuri'un da al'ummar Kamaru suka kada, yayin da dan adawa, Tchiroma Bakary ya biyo masa baya.
Tun kafin sanar da sakamakon hukuma Bakary ya sanar da cewa ya lashe zaben kasar, lamarin da ya jawo barkewar zanga-zanga a Kamaru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
