Abin Mamaki: An Samu Jirgin Saman da Ya Bata bayan Shekara 13 ana Nemansa
- Kamfanin Air India ya amince cewa ya sake gano wani jirgin fasinja na Boeing da ya ɓata tun shekarar 2012 a filin jirgin saman Kolkata
- Bayan gano jirgin saman, hukumomin masu lura da filin jirgi sun kakaba masa tarar ajiye jirgi mai yawa da ta kai kusan Rupee miliyan 10
- Rahoton ya sake tayar da tambayoyi kan tsarin adana bayanai da kulawa da kadarorin kamfanonin jiragen sama a Indiya da ma duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
India – Bayan shafe sama da shekaru 10 ana ɗaukar shi a matsayin jirgin da ya ɓace, kamfanin Air India ya gano wani jirgin fasinja na Boeing 737-200 da ya ɓace daga jerin kadarorinsa tun 2012.
Gano jirgin ya zo ne bayan da filin jirgin saman Kolkata ya nemi kamfanin da ya zo ya cire jirgin daga inda aka bar shi.

Source: Twitter
Rahoton the Sun UK ya nuna cewa jirgin ya shafe shekaru 13 yana ajiye a filin jirgin saman ba tare da an kula da shi ba, lamarin da ya jawo wa Air India tarar kuɗin ajiye jirgi mai yawa.
Yadda jirgi ya ɓata tsawon shekara 13
Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye jirgin Boeing 737-200 a filin jirgin saman Kolkata tun 2012, amma daga bisani sunan jirgin ya ɓace daga kundin bayanan Air India.
Jirgin ya kasance mallakin Indian Airlines ne tun farko, wani kamfani mallakin gwamnati da ya haɗu da Air India a 2007.
Bayan haɗewar kamfanonin biyu, an bayar da jirgin haya ga hukumar wasikun Indiya, inda aka sauya shi daga jirgin fasinja zuwa na ɗaukar kaya.
Daga bisani, an cire shi daga rajistar zirga-zirga a shekarar 2012, abin da ya ƙara rikitar da bayanansa a hukumance.
Shugaban Air India, Campbell Wilson, ya bayyana cewa an dade da daina amfani da jirgin domin ayyukan India Post, kuma kuskuren adana bayanai ya sa ba a saka shi cikin wasu muhimman takardu ba.
An ci tarar jirgin da ya bata a kasar India
Bayan filin jirgin saman Kolkata ya tuntubi Air India, kamfanin ya amince da mallakar jirgin tare da biyan tarar da aka kakaba masa.
The Independent ta rahoto cewa hukumar filin jirgin ta tabbatar da cewa Air India ta biya dukkan kuɗin ajiye jirgi da kula da shi da suka taru tsawon shekara 13.
An sayar da jirgin mai shekaru 43 sannan aka mika shi zuwa Bengaluru mako biyu da suka gabata. A can ne za a yi amfani da shi domin horas da ma’aikatan jirgi, maimakon sake dawo da shi aikin zirga-zirga.

Source: Getty Images
Jirgin Boeing 737-200 nada dogon tarihi, inda ya yi aiki a kamfanoni daban-daban ciki har da Indian Airlines, Alliance Air da India Post kafin a dakatar da shi a 2012.
AES ta yi barazanar harbo jirage
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar AES ta yi barazanar harbo jiragen sama da suka keta kasashenta ba tare da izini ba.

Kara karanta wannan
UAE: Daular Larabawa ta gamu da mummunan iftila'i, al'amura sun tsaya cak a birane
Kungiyar da ke kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ta ce shiga sararin samaniyarta ba tare da izini ba take doka ne.
Shugabannin sun yi barazanar ne bayan Burkina Faso ta rike jirgin Najeriya da wasu sojojin kasar 11 a kwanakin baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

