Wata Sabuwa: Donald Trump Ya Janye Jakadan Kasar Amurka daga Najeriya
- Shugaba Donald Trump ya janye jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, a wani mataki da ya shafi kasashe da dama a duniya, musamman a Afrika
- Rahotanni sun nuna cewa wannan umarni ya shafi fiye da kasashe 20, lamarin da ya haifar da rade-radi kan sabbin tsare-tsaren diflomasiyyar Amurka
- Janye jakadun na zuwa ne yayin da dangantakar Amurka da Najeriya ke fuskantar kalubale, duk da kokarin bangarorin biyu na karfafa hadin gwiwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yanke shawarar janye Richard Mills daga mukaminsa na jakadan Amurka a Najeriya.
Matakin na daga cikin wani shiri da ya shafi janyewar jakadu daga kasashe sama da 20, inda rahotanni suka nuna cewa Afirka ce ta fi fuskantar tasirin wannan sauyi.

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa masu lura da al’amuran kasa da kasa na kallon matakin a matsayin wani sabon salo da gwamnatin Trump ke dauka wajen sake tsara alaka da kasashen duniya.
Donald Trump ya janye jakadan Amurka a Najeriya
Najeriya na cikin kasashe 15 na Afirka da aka janye jakadunsu a wannan sauyi. Sauran kasashen sun hada da Aljeriya, Burundi, Kamaru, Cape Verde, Gabon, Côte d’Ivoire, Masar, Madagascar, Mauritius, Nijar, Rwanda, Senegal, Somalia da Uganda.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki ya zo ne ba tare da bambanci tsakanin manyan kasashe da kananan kasashe ba, lamarin da ke nuna cewa sauyin ya shafi yankuna daban-daban na nahiyar Afirka baki daya.
The Cable ta rahoto cewa janyewar ta haifar da tambayoyi kan yadda Amurka za ta ci gaba da tafiyar da hulda da wadannan kasashe a nan gaba.
An janye jakadun Amurka a wasu kasashe
Ba Afirka kadai ba ce ta fuskanci wannan sauyi. A yankin Asiya da Pacific, kasashe irin su Fiji, Laos, Marshall Islands, Papua New Guinea, Philippines da Vietnam sun shiga jerin kasashen da Trump ya janye jakadu.
Haka nan a Turai, kasashe kamar Armenia, Macedonia, Montenegro da Slovakia sun fuskanci irin wannan mataki, yayin da Guatemala da Suriname suka shiga jerin kasashen da abin ya shafa a yankin Amurka ta Yamma.
Masu sharhi na ganin cewa wannan ya nuna yadda sauyin ke da fadi kuma ya shafi kusan dukkan manyan yankunan duniya.
Alakar Jakadan Amurka da Najeriya
An tabbatar da Richard Mills a matsayin jakadan Amurka a Najeriya a watan Mayun da ya gabata, kuma janyewarsa na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar sanyi a dangantakar kasashen biyu, musamman kan batun biza da matsalolin tsaro.
Duk da haka, bangarorin biyu na ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin karfafa alaka. A makon da ya gabata, Mills ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, domin tattauna hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa ana dab da cimma wata yarjejeniya kan tsarin tsaro na hadin gwiwa, duk da wannan sauyi da aka samu a fagen diflomasiyya.
Shugaba Trump ya jawowa Najeriya asara
A wani labarin mun kawo muku cewa Najeriya ta tafka asarar kusan Naira tiriliyan 1 a saboda harajin Donald Trump.
Cibiyar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa an samu koma baya sosai a kan kayan da ake fitarwa daga Najeriya zuwa Amurka.
Idan aka kwatanta da yadda Najeriya da samu riba a 2024 da 2025, NBS ta ce kusan asarar Naira tiriliyan 1 aka yi a bana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


