Autria: Majalisa Ta Haramta Sanya Hijabi ga Yan Mata a Makarantu

Autria: Majalisa Ta Haramta Sanya Hijabi ga Yan Mata a Makarantu

  • Majalisar dokoki a ƙasar Austria ta amince da sabuwar doka da ta haramta sanya hijabi ga yan mata Musulmi
  • Gwamnati ta ce dokar ba ta nuna wariya ba, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce tana ƙara nuna kyamar Musulunci
  • Masu adawa sun gargadi cewa dokar za ta janyo wariya da kaskantar da ’yan mata, tare da lalata haɗin kan al’umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Vienna, Austria - Majalisar wakilan ƙasar Austria ta amince da wata sabuwar doka da ta haramta sanya hijabi a makarantu.

Sabuwar dokar ta samu amincewa ne da rinjayen ƙuri’u a zaman majalisar wacce ta haramta sanya hijabin ga yan mata a makarantu.

Austria ta haramta sanya hijabi a makarantu
Ministan hadin kai a Ausria, Claudia Plakolm. Hoto: Leonhard Foeger.
Source: Facebook

An haramta sanya hijabi a makarantun Austria

Rahoton Aljazeera ya ce kotun tsarin mulki ta taɓa soke irin wannan doka a baya saboda nuna wariya ga Musulmai.

Kara karanta wannan

An tsorata Bello Turji ya mika wuya bayan sojoji sun kashe mataimakinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karkashin sabuwar dokar, ’yan mata ƙasa da shekara 14 ba za su sake sanya gyale da ke rufe kai bisa al’adar Musulunci ba a dukkan makarantu.

Dokar ta tanadi tara daga Yuro 150 zuwa 800 ga iyayen yara idan suka ƙi bin ka’ida.

A shekarar 2019, gwamnatin Austria ta kafa dokar hana sanya gyale ga yara ƙasa da shekara 10 a makarantu, amma kotun tsarin mulki ta soke ta a 2020.

A lokacin, kotun ta ce dokar ta nuna wariya ga Musulmai kuma ta sabawa wajabcin gwamnati na kasancewa tsaka-tsaki a harkar addini.

An haramtawa yan mata sanya hijabi a makarantu
Dalibai sanye da hijabi zuwa makaranta. Wannan hoto bai da alaka da labarin, an sanya shi ne a matsayin misali. Hoto: Getty Images.
Source: UGC

Yadda majalisa ta amince da dokar

Sai dai gwamnatin yanzu ta ce ta yi iyakar ƙoƙarinta domin tabbatar da cewa sabuwar dokar za ta tsaya daram a gaban kotu.

Dokar ta fito ne daga kawancen jam’iyyu uku masu mulki, a lokacin da ake samun ƙaruwa a kyamar baƙin haure da Musulunci a ƙasar.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi: "Babu ruwan Kirista da shari'ar Muslunci"

Jam’iyyar ’yan ra’ayin rikau ta Freedom Party ta goyi bayan dokar, har ma tana son a faɗaɗa ta shafi dukkan ɗalibai da ma’aikatan makarantu.

Ministar Haɗin Kan Al’umma, Claudia Plakolm, ta bayyana gyalen yara a matsayin “alamar danniya”, cewar rahoton BBC.

Musulmi, kungiyoyi sun soki dokar

Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun soki dokar, Amnesty International ta ce dokar za ta ƙara ƙarfafa yanayin wariya da kyamar Musulmai.

Kungiyar IGGOe, wadda ke wakiltar Musulmai a Austria, ta ce dokar na barazana ga haɗin kan al’umma, tana ƙara ware yara maimakon ƙarfafa su.

Masana sun ce dokar na nuna yadda ra’ayin kyamar Musulunci ya zama ruwan dare a Austria, duk da cewa ba gwamnatin ’yan rikau kaɗai ce ta amince da ita ba.

Majalisa a Tajikistan ta haramta sanya hijabi

A baya, kun ji cewa Majalisar dokoki ta kasar Tajikistan ta amince da wani kudurin doka na haramta sanya hijabi ga mata Musulmi a kasar.

'Yan majalisar sun ce hijabi "bakin tufafi" ne da ke da alaka da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Kara karanta wannan

An ƙara yawan ƴan sanda a Adamawa don hana faɗan kabilanci

Gwamnatin Tajik karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da kudirin dokar da ya haramta yara yin bukukuwan Sallah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.