Trump Ya Tsokano Rigima, Amurka Ta Tare Jirgin China a hanyar Iran

Trump Ya Tsokano Rigima, Amurka Ta Tare Jirgin China a hanyar Iran

  • Rahoto ya nuna cewa sojojin Amurka sun kai samame kan wani jirgin da ya dauko kaya da ke tafiya daga China zuwa Iran
  • An ce Amurka kwace wasu kaya da Iran za ta yi amfani da su a cikin jirgin, duk da cewa kayayyakin ba na soji ba ne kadai
  • China ta soki matakan Amurka kan kwace jiragen ruwa, tana mai cewa takunkumanta kan Iran ba su da tushe a dokar duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun kai samame kan wani jirgin kaya da ke kan hanyarsa daga China zuwa Iran.

An ce hakan wani mataki ne da ake ganin yana kara tsaurara matsin lambar da gwamnatin shugaba Donald Trump ke yi a teku.

Kara karanta wannan

Abba ya yi ta maza, ya murkushe yunkurin Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano

Wani jirgin ruwa da Donald Trump
Donald Trump da wani jirgin ruwa a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Wall Street Journal ya ce wasu jami’an tsaro da ba a ambaci sunansu ba sun tabbatar da cewa an hau jirgin ne a tekun kusa da Sri Lanka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta kwace jirgin China zuwa Iran

Rahoton ya ce sojojin Amurka sun hau jirgin ne daga nisan daruruwan kilomita daga kasar Sri Lanka, inda dakarun musamman suka aiwatar da aikin.

Al-Jazeera ta ce wannan ne karon farko cikin shekaru da dama da Amurka ta tsayar da jirgin kaya da ke tafiya kai tsaye daga China zuwa Iran.

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kwace wasu kayayyaki da ake ganin na iya taimakawa Iran wajen kera makamai.

Sai dai jami'in ya jaddada cewa kayayyakin na da amfani biyu, wato ana iya amfani da su a harkokin soja da na farar hula.

Bayan kwace kayayyakin, an bar jirgin ya ci gaba da tafiyarsa, abin da ya nuna cewa ba a tsare jirgin gaba daya ba a lokacin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wani bam da aka dasa a kan titi ya tashi da mutane a Zamfara

Takunkumi kan Iran da martanin kasashe

Iran na ci gaba da kasancewa karkashin tsauraran takunkumin tattalin arziki daga Amurka, lamarin da ke kara tsananta dangantakarta da Washington.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Iran da China ba su fitar da martani kai tsaye ba ga abin da ya faru a Nuwamban 2025.

Jagoran addini na kasar Iran
Jagoran addini na kasar Iran, Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Sai dai China, wadda ke daya daga cikin manyan abokan kasuwancin Iran, ta dade tana sukar takunkuman Amurka, tana mai cewa ba su da inganci a karkashin dokar kasa da kasa.

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya yi Allah wadai da kwace wata tankar mai a gabar tekun Venezuela, wadda aka kai zuwa wani tashar jiragen ruwa a Texas.

Lamarin ya faru makonni kafin Amurka ta kwace wata tankar mai a gabar tekun Venezuela, abin da ke nuna sabon salo na matakan tsaro da Washington ba ta dauka tsawon shekaru ba.

Amurka ta kwace man Najeriya a teku

Kara karanta wannan

Amurka: Trump ya kwace babbar tankar mai mallakar kamfanin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta kwace wata tankar mai da ke da alaka da wani kamfanin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaron ruwa da sojojin Amurka ne suka kwace tankar ana tafiya da ita cikin teku.

Wasu hukumomi a Najeriya sun ce sai sun samu cikakken bayani game da lamarin kafin su yi karin haske ga al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng