Rawar da Faransa Ta Taka wajen Tarwatsa Masu Yunkurin Juyin Mulki a Benin
- Gwamnatin Faransa ta tabbatar da bada goyon baya ga Benin wajen dakile yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka ƙaddamar a ranar Lahadi
- A cewar fadar shugaban Faransa, an tura bayanan leƙen asiri da wasu taimakon dabaru domin karfafa dakarun Jamhuriyyar Benin a lokacin matsalar
- Ana danganta wannan rikici da irin yadda yankin Yammacin Afrika ke fama da juyin mulki a ƙasashe makwabta da ke girgiza tsarin dimokuraɗiyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France – Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa ta bai wa ƙasar Benin taimakon bayanan leƙen asiri da dabarun aiki domin dakile yunƙurin juyin mulki da aka yi ƙoƙarin kaddamarwa a ranar Lahadi.
Wannan bayanin ya fito ne daga jami’an fadar shugaban Faransa, wadanda suka tabbatar da cewa haɗin gwiwar ta kasance cikin matakan gaggawa na yankin ECOWAS.

Source: Twitter
Rahoton Reuters ya ce bayanan leƙen asiri da Faransa ta raba ba wai ga Benin kaɗai ba ne, har da Najeriya wadda ta tura jiragen yaki da sojojin ƙasa bayan gwamnatin Benin ta nemi taimako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar shugaban Benin, Patrice Talon, gwamnatin sa tare da rundunar sojin ƙasar sun dakatar da wasu sojoji da suka yi yunkurin hambarar da shi daga kujerar mulki, lamarin da ya ce dole ne a hukunta masu hannu a ciki.
Juyin mulki: Taimakon Faransa ga Benin
Jami’in shugaban Faransa ya bayyana cewa taimakon da suka bayar ya haɗa da sa ido, lura da yanayi, da wasu dabaru.
Ya ce wannan mataki yana cikin ƙoƙarin yankin ECOWAS na tabbatar da tsaro da kare tsarin mulkin dimokuraɗiyya a Yammacin Afrika.
Rahoton Arab News ya nuna cewa ya bayyana cewa:
“Mun bayar da tallafi ta fuskar sa ido da gano bayanai da dabarun aiki domin taimakawa dakarun Benin su dakile tashin hankalin.”
Sai dai duk da tabbatar da taimakon Benin, Faransa ta ƙi bayani dalla-dallai kan yadda aka gudanar da agajin da ta kai.
An tabbatar da cewa shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi magana da shugabannin Najeriya da Benin a karshen makon da ya gabata domin tattauna batun tsaro da kuma matakan da ake ɗauka.

Source: Facebook
Dalilin neman yin juyin mulki a Benin
Rahotanni daga Benin sun nuna cewa yankin Arewacin ƙasar ya yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda, musamman a watan Janairu da Afrilu, inda aka kashe sojoji da dama.
Masu yunkurin juyin mulkin sun yi ikirarin cewa rashin tsaro a Arewacin ƙasar ne ya sa suka nemi ƙoƙarin karɓe mulki.
Sai dai hukumomin Benin da abokan haɗin gwiwarsu na ketare sun bayyana wannan dalili a matsayin abin da ba ya da tushe, domin cibiyoyin tsaro na ƙasar na aiki domin shawo kan matsalar.
A ƙarshe, jami’an fadar shugaban Faransa sun jaddada cewa yanayin tsaro a yankin na buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen Yammacin Afrika.
Martanin Najeriya da ECOWAS a Benin

Kara karanta wannan
ADC ta zargi gwamnati da sakaci da tsaron Najeriya bayan hana juyin mulki a Benin
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta tura dakarunta da jiragen yaki zuwa Benin bayan samun bayanan gaggawa kan yunƙurin juyin mulki.
An ce matakin ya zama wani ɓangare na aikin haɗin gwiwa da ake yi domin kauce wa rikicin siyasa ya bazu zuwa sauran ƙasashen Afrika ta Yamma.
Najeriya da Benin sun bayyana cewa hadin kan su ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu da ECOWAS ke jagoranta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

