Abu Ya Girma: ECOWAS Ta Ayyana Dokar Ta Baci a Kasashen Yammacin Afirka
- Kungiyar ECOWAS ta sanya dokat ta baci a yankin Afirka ta Yamma bayan yunkurin juyin mulkik da sojoji suka yi a jamhuriyar Benin
- Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray ya bayyana hakan a taron gaggawa da kungiyar ta kira a birnin tarayya Abuja
- Ya ce kungiyar ba zata duba ido tana kalllo juyin mulki na kara yaduwa ba, wanda ta ce yana kara jawo barazanar tsaro a yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar raya kasashen yammacin Afirka watau ECOWAS ta shiga damuwa tare da fara daukar matakai domin kawo karshen yawaitar junyin mulki a kasashen da ke karkashinta
ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a fadin yankin Afirka ta Yamma a wani bangare na yunkurin dakile barazanar da ke addabar wannan yanki.

Source: Twitter
Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin zaman majalisar sulhu da tsaro ta ministoci karo na 55 da aka yi a Abuja, in ji Tribune Nigeria.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Benin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ECOWAS ta koka kan yawaitar juyin mulki
An kira taron ne saboda yawaitar juyin mulki da yunƙurin juyin mulki da ke faruwa a kasashen yammacin Afirka kwanan nan.
Touray ya ce wadannan abubuwa sun nuna cewa akwai bukatar a yi zurfin tunani kan makomar dimokuraḍiyya da kuma gaggawar zuba jari wajen kare tsaron al’umma.
Ya ce halin da ake ciki a Yammacin Afirka ya kai matakin “babbar barazana”, yana mai cewa daukar wannan matakin ya zama dole domin magance barazanar da juyin mulki ke haifarwa.
Ya jero matslolin da ke tunkarar Afirka ta Yamma ciki har da cikas a tsarin mika mulki ga farar hula a Guinea, raguwa ko takaita damar shiga zaɓe a wasu ƙasashe da kwararar ‘yan ta’adda, masu garkuwa, da ƙungiyoyin ta'addanci.
Omar Touray ya ce zaben yanzu a ƙasashe da dama a yammacin Afirka ya zama abin tayar da rikici maimakon samar da zaman lafiya, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Mafitar da ECOWAS ta hango
Shugaban hukumar ya yi kira da a riƙa yin taron majalisar sulhu akai-akai kuma a samar da kudi domin yaƙi da ta’addanci, ‘yan fashi da makami da kuma miyagun laifuka a kan iyakoki.
Ya ce lokaci ya yi da ECOWAS za ta dubi makomar dimokuraɗiyya a yankin, domin kiyaye tsarin mulki da zaman lafiya.

Source: Twitter
Alƙawarin ECOWAS ga jama’a
Duk da tsananin ƙalubale, Touray ya tabbatar da cewa kungiyar ba za ta yi biris da al’amuran yankin ba.
"Ba za mu yi shiru ba. Za mu ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da karfafa yankin don amfanin al’ummar mu,” in ji shi.
Juyin mulki: Gwamnoni sun yabi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun ce matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na dakile juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya ceci Najeriya
Gwamnonin sun ce gaggawar da Tinubu ya yi wajen dakile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya hana aukuwar babbar barazana ga tsaron Najeriya.
Kungiyar NGF ta kuma jinjinawa rundunar sojojin Najeriya bisa gaggawar da suka yi wajen taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Benin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

