Ekane: Jagoran 'Yan Adawa da Paul Biya a Kamaru Ya Rasu a Kurkukun Soja
- An sanar da rasuwar fitaccen ɗan adawar Kamaru mai hamayya da shugaban Paul Biya, Anicet Ekane bayan shafe kwanaki a hannun hukuma
- Ana zargin Ekane, wanda aka tsare tsawon kwanaki 38, ya rasu ne bayan matsananciyar wahalar numfashi da rashin kulawar likitoci ya tsananta
- Jam’iyyarsa ta MANIDEM ta kira rasuwarsa da “kisa”, lamarin da ta ƙara dagula rikicin siyasar da ta biyo bayan zaben shugaban ƙasar Kamaru
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yaounde, Kamaru – Fitaccen ɗan adawar Kamaru kuma shugaban jam’iyyar MANIDEM, Anicet Ekane, ya rasu a hannun sojoji a birnin Yaounde bayan kwana 38 da tsare shi.
Rasuwar tasa ta haddasa tashin hankali a fagen siyasar ƙasar, musamman ganin yadda ake kalubalantar sakamakon zaben watan Oktoban 2025.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta rahoto cewa Ekane, wanda ya kai shekaru 74, ya rasu ne da safe a ranar Litinin, kamar yadda iyalinsa da lauyoyinsa suka tabbatar.

Kara karanta wannan
Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama shi ne a ranar 24, Oktoban 2025 bayan ya goyi bayan Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaben duk da sanarwar gwamnatin da ta ce Paul Biya ya sake lashe wa’adin shugabanci.
Dalilin kama Ekane, dan adawa a Kamaru
Hukumomin Kamaru sun tuhume shi da “tayar da hankali da tawaye”, zarge-zargen da jam’iyyarsa ta bayyana a matsayin matakin siyasa da aka ɗauka domin tsoratar da 'yan adawa.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar MANIDEM ta ce tun farko ba a yi masa adalci ba tun lokacin da aka cafke shi ba tare da cikakken bayani ba.
Wani rahoton ya nuna cewa tun lokacin da aka kama shi a Douala, Ekane ya kasance cikin matsanancin yanayi na rashin lafiya, amma duk da haka ba a ba shi kulawa ta gaggawa ba kamar yadda lauyansa Emmanuel Simh ya bayyana.
Simh ya ce:
“Muna cikin baƙin ciki. Ekane bai aikata laifi ba, don haka muna buƙatar sanin dalilin kamasa da barinsa cikin wannan hali.”
Rashin lafiyar da ya yi kafin rasuwa
Babban dansa, Muna Ekane, ya shaida wa manema labarai cewa mahaifinsa ya yi fama da tsananin wahalar numfashi na tsawon mako guda kafin ya rasu.
Ya ce:
“Tsawon mako guda yana fama da wahalar numfashi; yana ƙoƙarin shakar iska.”
Yayin da ya ke bayani, Muna ya ƙara da cewa duk kokarinsu na sanar da jami’an tsaro bai haifar da wani mataki ba.
A ranar Lahadi kafin rasuwar tasa, jam’iyyarsa ta aika da bukatar gaggawa ga gwamnatin ƙasar domin a kai shi asibitin farar hula, inda ta gargadi cewa za ta ɗaura alhakin duk abin da ke faruwa a kan gwamnati.
Martanin gwamnatin Kamaru da ƙungiyoyi
Gwamnatin Kamaru ta ce an ba Ekane kulawa ta likitocin sojoji tare da hadin gwiwar likitocinsa na gida, tare da sanar da cewa an kaddamar da bincike.

Source: Facebook
Sai dai jam’iyyar MANIDEM ta bayyana rasuwar a matsayin “kisa”, yayin da tawagar Tarayyar Turai ta nuna “baƙin ciki matuƙa” a kafar X tare da kira da a saki duk waɗanda aka tsare ba bisa ka’ida ba tun bayan zaben.

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale
Dan adawar Kamaru, Bakary ya fake a Gambia
A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin jagororin 'yan adawa a kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya nemi mafaka a kasar Gambia.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin shugaba Paul Biya ta saka shi a gaba tana son kama shi bayan zaben shugaban kasa da aka yi a Kamaru.
Issa Bakary ya fara neman mafaka a jihar Adamawa da ake iyaka da Kamaru a Najeriya, inda jami'an tsaron kasarsa suka nemi Najeriya ta mika shi amma ta ki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
