'Third World': Najeriya da Kasashe 62 da Trump Zai Hana Mutanensu Zama a Amurka
- Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa zai dakatar da mutanen ƙasashen 'Third World' daga samun wurin zama a Amurka
- Masana sun ce kalmar 'Third World' ta fito ne tun lokacin yakin sunkuru, amma yanzu ana ɗaukarta matsayin kasashe masu tasowa
- A wannan rahoto, Legit Hausa ta jero kasashen da Trump ya ke nufi da 'Third World' ciki har da Najeriya, Indiya da kuma Iraq
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - A ranar 28 ga Nuwamba, 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa zai hana shigowar 'yan hijira daga kasashen 'Third World'.
Wannan mataki da Shugaba Donald Trump ke shirin dauka ya sake tayar da muhawara mai zafi kan ma’anar kalmar da kuma ko ta dace a ci gaba da amfani da ita.

Source: Twitter
Ma’anar kalmar “Third World” da sauyin da aka samu
Masana tarihi da tattalin arziƙi sun bayyana cewa kalmar Third World ta samo asali ne a lokacin Yakin Baka, kamar yadda aka karanta a wani littafi da aka wallafa a shafin hukumar NIMC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wancan lokacin, kalmar na nufin ƙasashen da ba su bi NATO ba ko kuma ƙungiyar Tarayyar Soviet.
Bayan rushewar Tarayyar Soviet a shekarun 1990, ma’anar kalmar Third World ta sauya. Aka dawo amfani da kalmar wajen nuni da:
- ƙasashen da ke fama da talauci mai tsanani
- matsalar tattalin arziki da rashin masana’antu
- karancin albarkatun rayuwa
Sai dai masana sun ce yau kalmar ta zama 'cin fuska', 'marar inganci', kuma bata dace a yi amfani da ita a kasashen duniya a wannan karni ba.
A maimakon haka, cibiyoyi kamar Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya suna amfani da kalmomi irin su:
- ƙasashen da ke tasowa
- ƙasashen da suka fi talauci
- ƙasashen da ke da ƙarancin kudin shiga
Jerin kasashen da ake kira “Third World”

Source: Facebook
A cewar wani rahoto na shafin World Population Review, ga jerin ƙasashen da ake ɗauka a matsayin 'Third World':
- Bhutan
- Iraq
- Eswatini
- Tajikistan
- Tuvalu
- India
- Bangladesh
- El Salvador
- Palestine
- Equatorial Guinea
- Cape Verde
- Namibia
- Guatemala
- Republic of the Congo
- Honduras
- Kiribati
- São Tomé and Principe
- Timor-Leste
- Kenya
- Ghana
- Nepal
- Vanuatu
- Laos
- Angola
- Micronesia
- Myanmar
- Cambodia
- Comoros
- Zimbabwe
- Zambia
- Cameroon
- Solomon Islands
- Uganda
- Ivory Coast
- Rwanda
- Papua New Guinea
- Togo
- Syria
- Mauritania
- Najeriya
- Tanzania
- Haiti
- Lesotho
- Pakistan
- Senegal
- Gambia
- DR Congo
- Malawi
- Benin
- Guinea-Bissau
- Djibouti
- Sudan
- Liberia
- Eritrea
- Guinea
- Ethiopia
- Afghanistan
- Mozambique
- Madagascar
- Yemen
- Sierra Leone
- Burkina Faso
- Burundi.
CPC: Trump zai sake tunani kan kasashe 19
A wani rahoton, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Donald Trump ta ce za ta sake nazari kan bakin da aka amince masu su zauna a kasar daga kasashe 19.
Hukumar kula da baki a Amurka (USCIS) ta ce ta fara duba damar da aka ba mutanen ƙasashe “masu babbar matsala”, bisa umarnin Trump bayan harbin sojoji.
Har ila yau, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dakatar da shigowar baki daga dukkan ƙasashe masu tasowa gaba ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


