Tashin Hankali: An Harbi Sojoji a Kusa da Fadar Shugaban Amurka, White House
- Sojoji biyu sun samu munanan raunuka bayan wani farmakin harbi da aka kai masu kusa da fadar White House ta kasar Amurka
- Rahoto ya nuna cewa an ɗauki matakin kulle fadar shugaban ƙasa na ɗan lokaci yayin da aka kara tsananta matakan tsaro a birnin Washington
- Shugaba Donald Trump ya yi tir da wannan hari wanda ya bar sojoji biyu cikin mawuyacin hali, ya ce za a hukunta wanda ya kai harin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington, DC – Rahotanni sun nuna cewa an rufe fadar shugaban kasar Amurka watau White House na wucin gadi a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025.
Hakan dai ya biyo bayan harbin da aka yi wa sojoji biyu masu tsaron kasa a kusa da fadar gwamnatin Amurka.

Source: Getty Images
Ministar harkokin tsaron cikin gida ta Amurka, Kristi Noem ce ta tabbatar da hakan a wani gajeren sako da ta wallafa a shafin X ba tare da ta yi karin bayani ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ’yan sandan Washington ta tabbatar da faruwar lamarin a layin kusa da fadar White House, abin da ya ƙara tsananta damuwa kan tsaro a babban birnin Amurka.
Lamarin ya faru a kusa da tashar metro ta Farragut, a daidai lokacin da ake cece-kuce kan umarnin Shugaba Donald Trump na tura ƙarin sojojin National Guard zuwa Washington.
An rufe White House na dan lokaci
Bayan harbin sojojin, an rufe Fadar Shugaban Ƙasa na ɗan lokaci, sai dai har yanzu gwamnatin Amurka ba ta fitar da cikakken bayani ba.
A lokacin da wannan lamari ya faru, Shugaba Trump yana Florida domin shirye-shiryen biki da aka saba yi a duk shekara.
Sai dai hukumomi sun tabbatar da cewa:
"An harbi sojoji biyu kuma suna cikin mummunan yanayi, an kuma kai mutum uku zuwa asibiti sakamakon wannan farmaki."
Wani rahoton AFP daga wurin ya ce an ji “harbe-harbe masu ƙarfi” sannan aka ga jama’a na gudu daga yankin Farragut Square, wuri mai cunkoso kusa da White House.
Shugaba Trump ya yi tir da harin
Da yake martani a shafinsa, Trump ya ce:
"Wanda ya harbi sojojin mu biyu, da ke kwance suna jinya a asibiti cikin mawuyacin hali, shi ma ya samu munanan raunuka, kuma za a hukunta shi da hukunci mai tsanani.”
Wata mai magana da yawun shugaban Amurka ta tabbatar da cewa an sanar da Trump rahoto nan take game da “abin takaici” da ya faru.

Source: Getty Images
Angela Perry, wata mata mai shekara 42 da ke tare da ’ya’yanta a cikin mota lokacin faruwar harin, ta ce:
“Mun ji harbe-harbe, muna tsaye muna jiran fitilar ba da hannu, haka aka ci gaba da harbe-harbe ba kakkautawa, sannan muka ga mutane na gudu.
Amurka za ta taimakawa Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta bayyana shirinta na aiki tare da Najeriya wajen magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.
Fadar shugaban kasan ta ce Amurka za ta samar da karin kayan leken asiri, kayan yaki da sauran kayan aiki domin karfafa ayyukan yaki da ’yan ta’adda a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan taron tattaunawa a makon da ya gabata tsakanin wata babbar tawagar Najeriya da jami’an gwamnatin Amurka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


