Babbar Magana: Sojoji Sun Kara Yin Juyin Mulki a Afirka, Sun Kama Shugaban Kasa

Babbar Magana: Sojoji Sun Kara Yin Juyin Mulki a Afirka, Sun Kama Shugaban Kasa

  • Sojojin Guinea-Bissau sun sanar da cewa sun karɓi cikakken iko a ƙasar bayan kwanaki uku kacal da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa
  • Rahotanni sun nuna cewa tun da safiyar yau Laraba, aka ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, sojoji sun mamaye manyan hanyoyi
  • Dakarun sojin sun karanta sanarwa daga Babban Hedikwatar Soji a Bissau, babban birnin kasar bayan sun gama kwace iko

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Guinea-Bissau - Rahotanni da ke shigowa yanzu haka daga kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa sojoji sun kifar da gwamnatin kasar.

Dakarun rundunar sojin sun sanar da cewa sun karbe ragamar mulki gaba daya tare da dakatar da duk wani abu da ya shafi zaben da aka yi nan take.

Umaro Sissoco Embaló.
Hambararren shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló Hoto: Umaro Sissoco Embaló
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun da sanyin safiyar yau Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025 aka ji karar harbe-harbe bindigogi a kusa da fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Jira ya kare: Shugaba Tinubu ya nada jakadu bayan fiye da shekara 2 a mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun karanta jawabin karbe mulki

Guinea-Bissau dai kasa ce da tarihi ya nuna cewa tana yawan fama da lamarin juyin mulkin sojoji a kai a-kai.

Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu, dakarun sojoji cikin kayan aiki dauke da makamai da shirin ko ta kwana sun mamaye babbar hanyar da ta kai zuwa fadar shugaban ƙasa.

Rundunar sojojin ta fito ta bayyana cewa ta karɓi cikakken iko a ƙasar, tare da dakatar da tsarin zaɓe da kuma rufe dukkan iyakokin Guinea-Bissau.

Wannan juyin mulki na zuwa kwana uku bayan zaben ’yan majalisa da na shugaban ƙasa da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

Sojojin sun sanar da kwace ikon ne ta hanyar karanta wani jawabi daga hedikwatar rundunar soji da ke cikin babban birnin ƙasar, Bissau, kamar yadda The Africa Report ta rawaito.

Sojoji sun kama Shugaba Embaló

Shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló ya tabbatar cewa an cafke shi da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

A hirarsa da Jeune Afrique, Shugaba Embaló ya ce an kama shi ba tare da amfani da tashin hankali ba, yana mai cewa:

“Manyan hafsoshin soji ne suka jagoranci wannan aiki, kuma abin da suka yi yunƙurin juyin mulki ne.”

Embaló ya riga ya ayyana cewa ya samu nasara a zaben shugaban ƙasa da aka yi ranar Lahadi, inda ya ce ya samu 65% bisa bayanin da tawagarsa ta tattara.

Umaro Sissoco Embaló.
Dakarun sojoji tare da shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló Hoto: Umaro Sissoco Embaló
Source: Facebook

Sauran wadanda sojoji suka kama sun hada da Janar Biaguê Na Ntan, Babban hafsan rundunar sojoji, mataimakinsa, Janar Mamadou Touré da Ministan harkokin cikin gida, Botché Candé.

Tarihin juyin mulki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa a tarihin Najeriya, an yi wa gwamnatocin farar hula har da na soja juyin mulki saboda wasu zarge zarge.

Manjo Patrick Chukwuma, wanda aka fi sani da Kaduna Nzeogwu, yana cikin jagororin juyin mulki na farko a Najeriya a ranar 15 ga Janairu 1966, bayan shekaru shida da samun 'yancin kai.

Bayan wannan juyin mulki an yi wasu da dama a tarihin Najeriya, mun tattaro muku su gaba daya a wannan rahoton.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262