Isra'ila Ta Kaddamar da Mummunan Hari, Ta Kashe Babban Hafsan Sojojin Hezbollah
- Wani mummunan harin sama da Isra'ila ta kai Lebanon ya hallaka babban hafsan sojojin Hezbollah, Hassan Tabtabai
- Kisan Tabatai na zuwa ne lokacin da Hezbollah ke fuskantar matsin lamba daga Amurka bayan shekara da tsagaita wuta
- Rahoto ya nuna cewa Tabtabai ya zama hafsan sojoji ne bayan Isra'ila ta kashe shugabannin Hezbollah a 2024
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lebanon - Isra’ila ta sanar da kashe babban kwamandan Hezbollah, Hassan Ali Tabatabai, a wani harin jirgin sama.
An ce Isra'ila ta kai harin ne a kan wani gida a unguwar Haret Hreik da ke Kudancin Beirut, ranar Lahadi, inda Tabatabai ke ciki.

Source: Getty Images
Isra'ila ta kashe hafsan sojojin Hezbollah
Sojojin Isra’ila sun bayyana Tabatabai a matsayin “Hafsan sojoji” na Hezbollah, kamar yadda rahoton The New York Times ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga baya Hezbollah ta tabbatar da mutuwar Tabatabai, tana mai cewa yana daga cikin manyan kwamandojin ta na soja.
Manyan sojojin da aka kashe tare da Tabatabai sun hada da Ibrahim Ali Hussein, Rifaat Ahmed Hussein, Mustafa Asaad Barrou da Qassem Hussein Barjawi.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta kuma rahoto cewa mutane 28 sun jikkata a harin, yayin da sojojin Isra'ila suka fitar da bidiyo na harin.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan hari shi ne mafi girma tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2024.
Matsin lambar Amurka da fargabar barkewar yaki
Tun bayan rattaba hannu kan tsagaita wutar da aka cimma a watan Nuwamba 2024, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare daban-daban a kudancin Lebanon, wadanda ta ce ana nufin sansanonin Hezbollah ne.
Sai dai hare-haren sun kashe fararen hula da jami’an tsaro na Lebanon. Duk da haka, Hezbollah ba ta mayar da martani ba saboda matsin lambar Amurka.
Yanzu haka Amurka ta ba gwamnatin Lebanon wani matsakaicin lokaci domin tilasta wa Hezbollah mika makamai.
Wannan matsin lamba, tare da hare-haren Isra’ila, na barazana ga tsagaita wutar da ta kawo karshen yakin 2024, wanda ya jawo mutuwar sama da ’yan Lebanon 4,000.

Source: Getty Images
Tasirin hafsan sojin Hezbollah da aka kashe
Sojojin Isra'ila sun ce Tabatabai ya kasance sojan Hezbollah da ya shiga kungiyar a 1980, kuma ya rike manyan mukamai, ciki har da jagorantar rundunar Radwan, da ayyukan Hezbollah a Syria.
A yayin yakin kasashen biyu, rundunar sojin Isra'ila ta ce an nada Tabatabai matsayin shugaban shirya yakin Hezbollah, wanda zai tsara yadda lamura za su tafi a kungiyar.
A karshen 2024, bayan Isra'ila ta kashe shugabannin Hezbollah, aka nada Tabatabai a matsayin kwamandan yaki da Isra'ila, in ji rahoton Times of Israel.
Bayan gama yakin Isra'ila da Hezbollah a Nuwambar 2024, an nada Tabatabai matsayin hafsan sojojin kungiyar. Kuma shi ne ya sake farfado da rundunar sojin Hezbollah.
Nasrallah: Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce shi ne ya ba sojojin kasarsa umarnin kashe shugaban sojojin Hezbollah.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah ya dauko haramar sake gina karfin da Isa'ila ta kwace daga Hezbollah.
Shugaban ya ce kisan da aka yiwa Nasrallah, wani mataki ne mai muhimmaci ga Isra'ila domin samun nasara a yakin da take yi da kungiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


