Wani Kiristan Najeriya Ya Ragargaji Donald Trump a Taron Tsaro na Duniya
- Japheth Omojuwa ya ce kalaman Donald Trump game da Najeriya na iya janyo ƙarin matsalar rashin tsaro a kasar
- Yayin da ya ke bayani, J. J Omojuwa ya ce sam bai ji dadin maganganun Trump ba duk da kasancewarsa Kirista
- Omojuwa ya bukaci manyan ƙasashen duniya su tallafawa Najeriya cikin ladabi ba tare da ta’azzara lamuran kasar ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Marubuci kuma fitacce a kafofin sadarwa na zamani Japheth Omojuwa ya bayyana cewa maganganun shugaban Amurka Donald Trump game da Najeriya na iya taka rawa wajen ƙara tsananta matsalolin tsaro.
Ya yi wannan bayani ne yayin da yake tambaya ga Sanata Kevin Cramer na Amurka a taron tsaro na duniya da aka gudanar a Halifax, Canada.

Source: Twitter
Omojuwa, wanda shi ma memba ne a kwamitin Halifax, ya wallafa bidiyon bayanin da ya yi a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ban ji daɗin barazanar Trump ba” — Omojuwa
A matsayinsa na Kirista, ya ce ba ya daga cikin waɗanda ke ganin Kiristocin Najeriya sun samu kwarin gwiwa daga alkawarin Trump na cewa zai ba su kariya.
Sanata Cramer ne ya yi ikirarin cewa Kiristocin Najeriya “na iya jin daɗi” da matsayar Trump, kafin Omojuwa ya yi nasa martani.
A cikin abin da ya ce, Omojuwa ya bayyana cewa:
“Ban ji daɗin maganar Donald Trump ba. Ya kira Najeriya ƙasa wadda ta yi abin kunya."
Ya ci gaba da tambayar ko ƙasashe masu ƙarfi za su iya ba da taimako cikin ladabi ba tare da cutar da waɗanda suke so su tallafawa ba.
Ya ba da misalai da cewa:
“Misali, Amurka ta kutsa Libya. Hakan ya taka rawa wajen janyo tsanantar matsalolin ta’addanci da Najeriya da yankin Sahel ke fuskanta. Ba na so in shiga batun sauran kasashen da Amurka ta shiga, mu dai dawo Najeriya.”

Kara karanta wannan
Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus
Omojuwa ya ce tun bayan maganganun Trump kan Kiristocin Najeriya, an yi garkuwa da Kiristoci a wuraren ibada a Arewa maso Yamma, tare da cewa:
“An kuma yi garkuwa da dalibai Musulmai. Ba na cewa maganganun Trump ne sanadi, amma akwai alaƙa tsakanin lokacin da ya yi furucin da kuma ƙaruwar harin ta’addanci.”
The Cable ta rahoto ya ce dole ne a yi magana game da Najeriya cikin mutuntawa:
“Akwai ƙa’idojin hulɗa. Akwai tsarin duniya na bin doka. Don haka akwai bukatar a yi magana kan Najeriya cikin mutunci.”

Source: Getty Images
Batun yarjejeniyar makamai da Najeriya
Omojuwa ya kuma tabo gazawar yarjejeniyar makamai tsakanin Amurka da Najeriya wadda ya ce ta raunana ƙoƙarin yaki da ta’addanci.
Ya tambaya:
“Shin ba za a iya taimaka wa Najeriya cikin ladabi ba, ba tare da ƙara ta’azzara al’amura ba, kuma ba tare da wulakanta Kiristoci da Musulman Najeriya ba?”
Sanata Cramer ya amsa da cewa akwai hanyoyi mafiya dacewa wajen yin magana:
“Kalmomi na da tasiri. Yin su da taushi ya fi amfani fiye da yin magana cikin tsauri.”
Kiristoci sun ce ana gallaza musu a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutanen Iran da suka koma addinin Kirista sun koka kan yadda ake mu'amala da su a Amurka.
Wasu daga cikinsu sun bayar da labarin yadda aka muzguna musu ta hanyar fatattakarsu ba tare da sanar da su ba.
Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka, Donald Trump ke barazanar kawo hari Najeriya da sunan kare Kiristoci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

