Ana Maganar Najeriya, An Gano yadda Trump ke Gallazawa Wasu Kiristoci a Amurka

Ana Maganar Najeriya, An Gano yadda Trump ke Gallazawa Wasu Kiristoci a Amurka

  • Wasu ’yan Iran da suka sauya addini zuwa Kiristanci sun ce an tursasa musu komawa gida duk da cewa sun nemi kariya daga gwamnatin Amurka
  • Rahotanni sun ce akwai rashin daidaito a yadda hukumomin Amurka ke tantance hatsarin da ke fuskantar wadanda suka nemi mafaka daga Iran
  • Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka ke cewa zai kai hari Najeriya domin kare mabiya addinin Kirista da ya ce ana yi wa kisan kare dangi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka - Mabiya addinin Kirista da suka fito daga Iran sun bayyana matsalolin da suke fuskanta a kasar Amurka.

Wani Kirista 'dan Iran ya bayyana yadda aka fatattake shi duk da cewa kotu ta ba shi kariya watanni biyar da suka gabata.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump yana wani jawabi a ofis. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

BBC ta rahoto cewa an ɗaure masa hannu da kafa, aka dauke shi cikin dare zuwa filin jirgin saman soji a Louisiana, tare da sanar da shi cewa za a fitar da shi daga ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya tsere ne daga Iran zuwa Amurka bayan tsangwama da ya ce an yi masa sakamakon shiga zanga-zangar Mahsa Amini da kuma sauya addininsa zuwa Kiristanci.

Duk da neman mafaka da ya yi, an tilasta masa hauwa jirgin da ke dauke da fiye da mutum 150 zuwa Managua, inda daga nan aka sake tura shi cikin wata hanya da zata dawo da shi Iran.

Yadda aka kori Kiristoci daga Amurka

A cewar hukumomin White House, duk wadanda aka maida gida an bi matakai kamar yadda doka ta tanada, kuma wasu daga cikinsu sun nemi a mayar da su da kansu.

Sai dai a cikin watan Satumba, an shirya wani jirgi na musamman zuwa Iran ta Qatar – abu da ba a saba yi ba tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji abin da ya hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka ya gana da Trump

An ɗaure wasu daga cikin wadanda suka shiga jirgin, kuma rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun rika tsare su yayin tafiya daga Qatar zuwa Tehran.

Daya daga cikin fasinjojin ya ce an yi musu tambayoyi kan zamansu a Amurka da kuma al’amuran addini.

Shafin ICC na Kiristoci ya ce Trump ya kori Kiristocin Iran 100 zuwa Costa Rica da Panama ba tare da sauraron korafinsu ba.

Yadda aka kori wata Kirista a Amurka

Daga cikin mutanen da ke cikin damuwa akwai matar wani mutum mai suna Ali, ɗan Iran da ya sauya addini kuma yake zaune a Amurka.

Ali ya bayyana cewa an mayar da matarsa Iran:

“Sun kori matata duk da cewa Kirista ce. Yanzu hukumar leƙen asirin Iran na bibiyar mu.”

Lauyoyi da ke kare su sun ce an yi kuskuren barin bayanai masu tsananin mahimmanci a cikin takardun wadanda aka kora.

Sun ce cikin kuskuren da aka yi har da dalilan sauya addini da matsalolin siyasa, wanda hakan zai iya jefa su cikin haɗari idan sun koma Iran.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya fadi hanyoyi 5 da Tinubu zai bi ya kawo karshen rashin tsaro

Jagoran addini na kasar Iran
Jagoran addini a kasar Iran, Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Wani lamari mai tayar da hankali ya faru da Marjan da Reza, wadanda dukkansu Kiristoci ne daga Iran da suka nemi mafaka a Amurka.

Jami’an ICE sun kama su a gidansu a Los Angeles, inda aka raba su zuwa cibiyoyi daban-daban. Marjan ta samu mafaka daga kotu, yayin da aka yanke hukuncin maida Reza wata ƙasa.

Fasto Ara Torosian, wanda ya shaida kamasu ya ce hukumar tsaron Amurka ta yi kuskure wajen kiran su marasa izinin zama, domin sun shigo ƙasar bisa tsarin jinƙai tare da samun izinin aiki.

Maganar 'yar majalisar Amurka kan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wata 'yar majalisar Amurka, Sara Jacobs ta yi magana kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Sara Jacobs ta yi Allah wadai da barazanar da Donald Trump ya yi game da kai hari Najeriya kan zargin kashe Kiristoci.

Ta ce kashe-kashen da ake a Najeriya ba lallai su kasance suna da alaka da addini ba, saboda haka bai kamata a yi maganar nuna karfin soja ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng