Nuhu Ribadu Ya Gana da Ministan Tsaron Amurka kan Barazanar Kawo Hari Najeriya

Nuhu Ribadu Ya Gana da Ministan Tsaron Amurka kan Barazanar Kawo Hari Najeriya

  • Malam Nuhu Ribadu ya gana da Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, da Shugaban Hafsoshin Tsaron Amurka, Janar Dan Caine
  • Wannan ganawa na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke ci gaba da kokarin warware matsalar da ta taso har Trump ya yi barazanar kawo hari
  • Rahotanni sun bayyana cewa Ribadu da manyan hafsoshin tsaron Amurka sun tattauna batutuwa masu muhimmanci a ranar Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, na ci gaba da tattaunawa da shugabannin tsaron Amurka kan barazanar kawo farmaki Najeriya.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi baranazar daukar matakin soji kan Najeriya saboda, a cewarsa, ya samu labarin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Malam Nuhu Ribadu.
Hoton mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Ribadu ya gana da hafsoshin tsaron Amurka

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Vanguard ta ruwaito cewa NSA Nuhu Ribadu ya gana da Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, da Shugaban Hafsoshin Tsaron Amurka, Janar Dan Caine, a jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta maida hankali kan barazanar Shugaba Donald Trump cewa zai tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yakar abin da ya kira cin zarafin Kiristoci.

A cewar ABC News, manyan hafsoshin tsaron Amurka biyu sun tabbatar da ganawa da Ribadu duk da babu taron a jadawalin ayyukansu na jiya Alhamis.

Me manyan jiga-jigan suka tattauna?

Bugu da kari, bayanai sun nuna cewa ba a bari 'yan jarida sun shiga wurin taron a Pentagon ba, alamar da ke nuna muhimmancin abubuwan da aka tattaunawa.

Hakan na zuwa ne bayan Trump, a farkon watan Nuwamba, ya umurci rundunar Pentagon da ta shirya kai hare-hare a Najeriya idan gwamnati a Abuja ta kasa dakile kisan kiyashin da ake wa kiristoci.

Batun ya samu karbuwa sosai a cikin ƙungiyoyin magoya bayan Trump a Amurka, ciki har da goyon bayan Sanata Ted Cruz da dan majalisa, Riley Moore.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jam'iyyar APC ta aika wasika zuwa majalisar dokokin Amurka

Barazanar Trump ta kawo hari Najeriya

A wani sako da Trump ya wallafa a ranar 1 ga Nuwamba, 2025 a shafinsa na sada zumunta, ya yi gargadi cewa:

“Idan Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da bari ana kashe kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi kuma wataƙila mu shiga wannan ƙasa, mu shafe ‘yan ta’adda gaba ɗaya.”

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa bayanan da Amurka ta samu ba na gaskiya ba ne.

Ganawar Ribadu da manyan hafsoshin tsaron Amurka wani bangare ne na ƙoƙarin warware sabani da inganta huldar diplomasiya tsakanin kasashen guda biyu.

Nuhu Ribadu da Sakataren tsaron Amurka.
Hoton NSA Nuhu Ribadu da sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth Hoto: @nuhuribadu
Source: Twitter

Tawagar Ribadu ta gana Riley Moore

A baya, kun ji cewa tawagar da Nuhu Ribadu ya jagoranta ta gana da dan majalisar Amurka, Riley Moore kan zargin wariyar addini a Najeriya.

A cikin wata sanarwa dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya fitar, ya tabbatar da ganawarsa da tawagar Najeriya, yana mai cewa tattaunawar ta kasance mai amfani.

Kara karanta wannan

Ribadu da manyan Najeriya sun isa Amurka, sun tattauna batun rashin tsaro

Daga cikin tawagar akwai Antoni Janar na tarayya, Lateef Olasunkami Fagbemi; hafsun tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede da Laftanar Janar EAP Undiendeye na rundunar leken asiri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262