Duniya za Ta Kafa Rundunar Tsaro a Gaza, Falasdinawa za Su iya Samun 'Yanci
- Majalisar dinkin duniya ta amince da kudurin Amurka da ke tanadin kafa gwamnatin wucin-gadi da rundunar tsaro ta duniya a Gaza
- Kudurin ya nuna cewa yanzu akwai yiwuwar samun “hanyar gaskiya” ta kafa ƙasar Falasdinu bayan aiwatar da sauye-sauye
- Hamas da wasu jami’an Isra’ila sun yi watsi da kudurin, suna cewa bai cika bukatun Falasdinu ba kuma yana ƙoƙarin kakabawa Gaza tsarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Majalisar tsaron majalisar dinkin duniya ta amince da wani sabon kuduri da Amurka ta gabatar wanda ke tanadar kafa gwamnatin wucin-gadi da kuma rundunar tsaro ta duniya a Gaza.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin tabbatar da tsagaita wutar aka ce an yi tsakanin Isra’ila da Hamas.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta ce kudurin, wanda ke cikin shirin zaman lafiya na shugaba Donald Trump, ya samu kuri’u 13 cikin 15.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai duk da yadda aka amince da kudirin, ƙasashen Rasha da China sun kaurace wa kada kuri’a a zaman.
Manufar kudirin da martanin Isra'ila
An bayyana cewa matakin na daga cikin muhimman abubuwan da ake fata za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Rahoton Washington Post ya ce kudurin ya ce:
“Yanayi na iya kasancewa a karon farko domin samar da hanya ta gaskiya ga samun ’yancin kai da kafa ƙasar Falasdinu”
Hakan zai yiwu ne bayan sakamakon sauye-sauyen da hukumar Falasdinu za ta aiwatar da su da kuma ci gaban gina Gaza.
Sai dai wannan wannan bangare ya fusata Benjamin Netanyahu, wanda ya ce ƙasarsa tana adawa da kafuwar ƙasar Falasdinu.
Ya ce:
“Za mu ci gaba da kawar makaman da suke Gaza, ko ta hanya mai sauƙi ko ta wata hanyar.”
A daya bangaren, ministan tsaron cikin gidan Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya je gaba, inda ya yi watsi da kudurin yana mai cewa:

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya
“Idan majalisar dinkin duniya ta goyi bayan kafa ƙasar Falasdinu, ya kamata a yi wa wasu jami’an hukumar Falasdinu kisan gilla.”
Muryoyin ƙasashen duniya game da Gaza
Kasashe da dama sun yi magana game da kudirin, inda jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya, Mike Waltz, ya ce:
“Wannan kuduri wani muhimmin mataki ne da zai bai wa Gaza damar bunƙasa a yanayi mai ba da kariya ga Isra’ila.”
Jakadan Aljeriya, Amar Bendjama, ya nuna godiya ga shugaban Amurka, yana mai cewa:
“Muna godiya ga Shugaba Trump, wanda jajircewar sa ta taimaka wajen kafa da kuma tabbatar da tsagaita wutar Gaza.”
Sai dai ya ƙara jaddada cewa:
“Ainihin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba zai tabbata ba tare da adalci ba, adalci ga Falasdinawa da suka dade suna jiran kafuwar ƙasarsu mai ’yanci.”

Source: Getty Images
Martanin Hamas kan kudirin Gaza
Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudurin, tana mai cewa bai cika hakkokin Falasdinawa ba. A cewarta:
“Kudurin bai amsa bukatun Falasdinawa ba, kuma yana ƙoƙarin kakabawa Gaza wani tsarin kula na ƙasashen duniya wanda Falasdinawa da kungiyoyin gwagwarmaya ba su so.”
Turkiyya na neman kama Netanyahu
A wani labarin, mun kawo muku cewa kasar Turkiyya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Wata kotun kasar ne ta bayyana haka a wani zama da ta yi, inda ta ce ya jagoranci kisan kiyashi a Gaza.
A martanin da ta yi, kasar Isra'ila ta yi Allah wadai da matakin tana mai cewa abubuwan da aka zargi Netanyahu da su ba gaskiya ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

