Rashin Imani: Dan Najeriya Ya Kashe Mahaifinsa, Ya Cakawa Kannnesa Wuka a Amurka

Rashin Imani: Dan Najeriya Ya Kashe Mahaifinsa, Ya Cakawa Kannnesa Wuka a Amurka

  • ’Yan sanda a New Orleans sun kama Chukwuebuka Eweni, bisa zargin kashe mahaifinsa, Farfesa Samuel Eweni
  • Eweni, wanda shi da iyayensa 'yan asalin Najeriya ya kuma raunata ’yan uwansa mata biyu, abin da ya girgiza al’umma
  • Yayin da ake zargin Eweni ya na da tabin hankali, an ce marigayin farfesa ne a jami'ar Southern University, New Orleans

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - An shiga tashin hankali a unguwar Pebble da ke New Orleans yayin da wani dan asalin Najeriya ya kashe mahaifinsa tare da jikkata 'yan uwansa.

An ce , Chukwuebuka Eweni kashe mahaifinsa, Farfesa Samuel Eweni sannan ya raunata ’yan uwansa mata biyu a cikin gidansu da daddare.

Dan Najeriya ya cakawa mahaifinsa wuka har lahira, ya ji wa kannensa mata rauni a Amurka
Farfesa Samuel Eweni, mutumin da dansa ya kashe a Amurka. Hoto: WWLTV
Source: UGC

“Abin ya zo ba zato ba tsammani” — ’Yan uwa

Rahotanni jaridar WWL Louisiana sun tabbatar da cewa marigayin, Samuel Eweni, farfesa ne na kimiyyar kwamfuta a jami'ar Southern University da ke New Orleans.

Kara karanta wannan

An bindige matashi a wajen jana'izar mahaifinsa bayan turnukewa da harbe harbe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangi sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici matuka, inda suka bayyana cewa Eweni na fama da matsalolin tabin hankali amma ba su san shi da tashin hankali a baya ba.

Daya daga cikin ’yan uwansa mata da ta ji rauni an sallame ta daga asibiti, yayin da dayar ke samun kulawar likitoci amma ana sa ran za ta warke.

An gano wanda ake zargi a Jefferson Parish

A cikin sanarwar da aka samu daga rundunar ’yan sanda ta New Orleans (NOPD), an tabbatar da cewa an gano Chukwuebuka Eweni a Jefferson Parish.

Hukumar ta ce:

“Chukwuebuka Eweni yana hannun jami’an tsaro, kuma ana duba lafiyarsa a wata cibiyar jinya.”

An ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:59 na dare ranar 11 ga Nuwamba, 2025.

A cewar NOPD, an samu kiran gaggawa cewa an yi “aikata kisan kai” ta hanyar yanka, wanda ake zargin rikicin cikin gida ne ya jawo hakan.

Kara karanta wannan

A.M Yerima: Tsohon jigon APC, Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike

Lokacin da jami’an suka isa, sun tarar da Farfesa Samuel Eweni cikin jini ba tare da alamun rai ba, sannan suka gano wasu mata biyu da raunukan wuka.

Masu bincike na sashen kisan kai na NOPD sun tabbatar da cewa Eweni shi ne wanda ya kashe mahaifinsa.
Motar rundunar 'yan sandan New Orleans da ke Amurka. Hoto: @NOPDNews
Source: Twitter

Laifukan da ake tuhumar dan Najeriya da su

Tun da fari, masu bincike na sashen kisan kai na NOPD sun tabbatar da cewa Eweni shi ne wanda ya aikata laifin, in ji rahoton Punch.

Bayan bincikensu ne suka samu takardar izinin cafke shi bisa laifuffukan, zargin kisan kai da zargin yunkurin kisan kai.

A sanarwar an ce, “Wannan wanda ake zargi ana ganin yana da makami kuma yana da matukar hadari.”

Hukumar ta ce ofishin Orleans Parish Coroner zai bayyana sunan mamacin a hukumance da kuma musabbabin mutuwa bayan autopsy da sanar da ’yan uwa na kusa.

Matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sandan Jigawa sun cafke wani matashi da ake zargi da daba wa mahaifinsa adda har ya mutu a ƙaramar hukumar Gwaram.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara, inda ake zargin matashin mai shekaru 20 ya kai wa mahaifinsa harin da ya jawo rasuwarsa.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun taso sojan da ya kalubalanci Wike a gaba, suna neman a kori matashin a aiki

Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya umarci a mayar da binciken lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID) da ke babban birni Dutse.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com