Amurka Da Saudiyya Za Su Kulla Wasu Sabbin Yarjejeniyoyi a Mako Mai Zuwa

Amurka Da Saudiyya Za Su Kulla Wasu Sabbin Yarjejeniyoyi a Mako Mai Zuwa

  • Shugaban kasan Amurka Trump zai gana da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman a makon da za a shiga
  • Majiya ta bayyana yadda aka tsara zaman da kuma ziyarar da Yariman zai kai a kasar Amurka kan wasu batutuwan tsaro da tattalin arziki
  • Tun farkon hawan Trump mulki yake kokarin tabbatar da ya kulla alaka mai karfi da kasashen larabawa, musamman Saudiyya, Qatar da UAE

Washinton, Amurka — Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ziyarar da Yariman Sarkin Saudiyya Mohammed bin Salman zai kai fadar White House mako mai zuwa za ta zarce taron aiki kawai.

Ya bayyana cewa, ziyarar za ta kasance a matsayin dama ta “girmama Saudiyya da Yarima,” a jawabin da ya yi cikin jirgin Air Force One.

Duk da cewa an ayyana ziyarar a matsayin ta aiki, wani babban jami’in gwamnatin ya ce White House na shirin karɓan baƙon da ɗabi’ar da ake tanada wa manyan baƙi na ƙasa.

Kara karanta wannan

Yar majalisa ta dura kan tsohon shugaban Amurka da ya saukakawa Najeriya kan addini

Abin da Saudiyya da Amurka ke ciki na yarjejeniya
Amurka da Saudiyya kan ziyarar MBS | Win McNamee - Hoton nan na ganawar Trump da MBS a baya cikin watan Mayun 2025
Source: Getty Images

Yadda tsarin ziyarar zai kasance

A ranar Talata, Yariman zai fara ziyarar da bikin tarba a South Lawn, sannan a yi masa maraba a South Portico.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan Trump zai karɓe shi a ofishinsa na Oval House domin ganawar bangarori biyu kafin su shiga dakin Majalisar Ministoci domin sa hannu kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da tsaro da aka shirya kammalawa tsakanin Amurka da Saudiyya.

Da yammaci, za a gudanar da liyafa a East Room ta White House, wadda Uwargidan Trump, Melania Trump, ta tsara.

A ranar Laraba kuma, ana sa ran shugabannin manyan kamfanoni da dama za su halarci taron Majalisar Kasuwanci ta Amurka da Saudiyya a Kennedy Center.

Alakar Trump da kasashen larabawa a yanzu

Duk da cewa ba a tabbatar da halartar Trump ba, jami’in ya ce akwai yiwuwar ya shiga taron kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Gulf ya kasance ginshiƙi a manufofin Trump na ketare a wa’adinsa na biyu, kamar yadda ya sha fadi a kalamansa.

Kara karanta wannan

Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa

A farkon manyan tafiye-tafiyensa na waje, ya ziyarci Saudiyya da UAE da Qatar, inda jiragen yaki na F-15 na Rundunar Sojin Sama ta Saudiyya suka raka Air Force One, kuma ya halarci liyafar kasa-da-kasa a wani muhimmin wurin UNESCO.

Yadda Trump ya aminta da Yariman Saudiyya

A cewar Trump yayin wani taro da Yarima a Riyadh:

“Ina gaskata cewa muna son juna ƙwarai."

Daga bisani ya bayyana Yarima Mohammed a matsayin “mutum mai ban sha’awa” kuma aboki na kut yayin ganawar ta su.

Trump dai na daga cikin shugabannin da ba su cika jituwa da kasashe da dama ba, ciki har da kasashen Afrika.

Barazanar Trump ga Najeriya

Idan ba ku manta ba, kwanakin baya ne shugaban Amurka Trump ya bayyana barazanar farmakar Najeriya bisa zargin ana yiwa kiristoci kisan gilla a kasar.

Najeriya dai kasa ce da ta dauki shekaru sama da 15 tana fama da rikicin hare-haren 'yan ta'adda, tun bayan barkewar rikicin Boko Haram.

Sai dai, masana da masu bibiyar lamaran yau da kullum sun shaidawa duniya cewa, babu wani lamari mai kama da yiwa kiristoci kisan gilla, inda kisan ya fi shafar Musulmai da dama a kasar, musamman a Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng