'Yan Majalisar Dokoki Sun Tsawaita Wa'adin Shugaban Kasa a Benin

'Yan Majalisar Dokoki Sun Tsawaita Wa'adin Shugaban Kasa a Benin

  • Majalisar dokokin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta tsawaita wa'adin shugaban kasa zuwa shekaru bakwai
  • Wannan mataki na zuwa ne yayin da kasar ke shirye-shiryen zaben shugaban kasa, wanda za a gudanar a shekarar 2026
  • Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin, wanda ke cikin wa'adi na biyu, ya sha nanata cewa ba zai nemi tazarce a zabe mai zuwa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jamhuriyar Benin - ’Yan majalisar dokoki na Jamhuriyar Benin sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki a ranar Juma’a, 14 ga watan Nuwamba, 2025.

Gyaran da yan Majalisar dokokin suka yi ya kunshi ƙara wa’adin shugaban ƙasa zuwa shekaru bakwai, kuma sau daya mutum yake da damar maimaita wa.

Shugaban Jamhuriyar Benin.
Hoton shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon Hoto: Patrice Talon
Source: Facebook

An kara wa'adin shugaban kasa a Benin

A cikin kuri’u mafi rinjaye 90-19, sabuwar dokar ta ayyana cewa shugaban ƙasa zai yi mulki na shekaru 7 kacal, kuma ana iya sabunta shi sau ɗaya tak, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mata 6 da suka sha ƙasa a zaben gwamna a zaɓukan Najeriya

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar dokoki ta fitar a ranar Asabar, 15 ga watan Nuwamba, 2025.

A rahoton Vanguard, sanarwar ta ce:

“Daga yanzu, bisa ga gyaran sashe na 42, zaɓabben shugaban ƙasa da al'umma suka kada wa kuri'unsu zai yi shekaru bakwai a gadon mulki wanda za a iya sabunta shi sau ɗaya tak.
"Babu wanda zai iya zama shugaban ƙasa fiye da wa’adin mulki biyu a rayuwarsa.”

Yan Majalisa sun tsawaita wa'adin ciyamomi

Bugu da kari, yan majalisar sun kuma tsawaita wa’adin mulki na shugabannin kananan hukumomi da kansiloli zuwa shekaru bakwai.

Wannan gyara na zuwa ne kafin zaben shugaban kasa da za a yi a 2026 a jamhuriyar Benin, kasar da ke magana da harshen Faransanci a Yammacin Afirka.

Shugaba Patrice Talon, wanda ya hau mulki tun 2016, yana kan wa’adinsa na biyu. Talon ya sha nanatawa a bainar jama’a cewa ba zai nemi wa’adi na uku ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da sake nada Buba Marwa shugaban NDLEA zuwa 2031

An dakile juyin mulki a Jamhuriyar Benin

Ko da yake Benin na da kwanciyar hankali a tsarin dimokuraɗiyya idan aka kwatanta da makwabtanta, a bara, an yi zargin cewa sojoji sun yi yunƙurin juyin mulki.

A cewar rahoto, an ga Oswald Homeky, tsohon ministan wasanni, ya na ba Djimon Tevoedjre, kwamandan rundunar kare shugaban kasa, jakunkuna shida na kuɗi da ke ɗauke da Saifa biliyan 1.5 (kimanin dala miliyan 2.5).

Patrice Talon.
Hoton shugaban jamhuriyar Benin, Patrice Talon da zauren Majalisar dokoki Hoto: Patrice Talon
Source: Facebook

Haka kuma, an zargi Olivier Boko, ɗan kasuwa kuma abokin Talon na dogon lokaci, da hannu a cikin shirin juyin mulkin.

A wancan lokaci, Boko ya fara bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2026.

Yan majalisar Amurka 31 na tare da Trump

A wani labarin, kun ji cewa 'yan majalisar dokokin Amurka 31 sun goyi bayan Shugaba Donald Trump kan matakin da ya dauka na sanya Najeriya a kasashen CPC.

Ƴan majalisar sun bayyana matakin a matsayin “na jarumta”, su na mai cewa hakan ya nuna damuwar Trump kan cin zarafi da kashe Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

ADC ta taso Shugaba Tinubu a gaba kan sabon bashin da zai kinkimo

A cewarsu, matakin da Trump ya ɗauka ya farfaɗo da muradun Kiristocin Najeriya da kuma tabbatar da Amurka a matsayin ƙasa mai kare ’yancin addini a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262