Yar Majalisa Ta Dura kan Tsohon Shugaban Amurka da Ya Saukakawa Najeriya kan Addini

Yar Majalisa Ta Dura kan Tsohon Shugaban Amurka da Ya Saukakawa Najeriya kan Addini

  • ‘Yan Majalisar Amurka Nancy Mace ta zargi gwamnatin Joe Biden da rage mahimmancin yancin addini musamman kan Najeriya
  • Mace ta ce tabbas Najeriya ta zama “daga cikin kasashe mafi hadari ga Kiristoci.” inda ake tauwe musu hakkin gudanar da addini
  • Matar ta yaba wa Donald Trump, tana cewa yana kokarin mayar da Najeriya cikin jerin kasashe da aka sanya karkashin CPC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wakiliyar Majalisar Dokoki ta Amurka, Nancy Mace, ta soki yadda tsohuwar gwamnatin Joe Biden kan yancin addini.

Mace ta yi magana kan batun ‘yancin addini a duniya, tana cewa Najeriya ta zama daya daga cikin kasashe mafi hadari ga Kiristoci.

An yabawa Trump kan barazana ga Najeriya
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Twitter

Yar majalisar ta bayyana haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar 2025.

Kara karanta wannan

AU ta mayar da martani ga Trump kan ikirarin ana kisan Kiristoci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar Trump da ya jawo magana a duniya

Wannan zargin ya biyo bayan kalaman Trump a watan da ya gabata, inda ya yi ikirarin cewa Kiristanci a Najeriya na fuskantar barazana mai tsanani daga kungiyoyin tsattsauran ra’ayi.

Trump ya wallafa a 'Truth Social' cewa “ana kashe dubban Kiristoci,” kuma ya ce ya sanya Najeriya cikin jerin CPC.

Haka kuma, Trump ya umarci ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta duba yiwuwar daukar matakin soja kan kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.

Dukan wadannan maganganun, gwamnatin Najeriya ta yi watsi da su, yayin da kasashen China da Russia suka bukaci Amurka ta mutunta ikon Najeriya.

An soki Biden da saukakawa Najeriya
Shugaba Donald Trump da Joe Biden. Hoto: Congresswoman Nancy Mace, Donald J Trump, Joe Biden.
Source: Facebook

Martanin yar majalisa kan gwamnatin Biden

Mace ta caccaki gwamnatin Biden kan cire Najeriya daga jerin kasashen da ake zargi da take hakkokin addinai.

Ta kuma kawo misali da gwamnatin Donald Trump, tana yabawa matakan da shugaban ya dauka wajen kare ‘yancin addini.

Kara karanta wannan

Jerin kungiyoyin duniya da suka karyata Trump kan zargin da ya yi wa Najeriya

A cewarta:

“A halin da ake ciki kuma, Shugaba Biden ya cire Najeriya daga jerin CPC.
“Shugaba Trump yana kokarin mayar da wadannan matakai. 45/47 na daga cikin shugabannin da suka fi tasiri a tarihin Amurka.”

Yadda Biden ya tsame Najeriya karkashin CPC

Wannan shi ne karo na biyu cikin shekaru biyar da aka sanya Najeriya cikin jerin CPC, Na farko ya kasance a 2020, a lokacin gwamnatin Trump, bisa zargin cewa akwai take hakkokin addini a Najeriya.

Sai dai gwamnatin Biden ta cire Najeriya daga jerin a watan Nuwamba 2021 duk da samun korafe-korafe daga wasu a wancan lokaci.

Wannan lamari ya jawo maganganu da martani daga kungiyoyi masana harkokin kasashen waje da tsaro da kuma wasu kasashe da ke ganin bai kamata a yi wa Najeriya mai yancin kanta barazana haka ba.

Trump: Dan majalisa ya sake gargadin Tinubu

A baya, an ji cewa dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya kuma gargadin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan barazanar Donald Trump.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla

Moore ya gargadi gwamnatin Najeriya da ka da ta raina nufin Shugaba Donald Trump wajen dakatar da kisan Kiristoci.

Ya ce Trump zai ɗauki matakai masu tsauri idan tashin hankalin ya ci gaba, yana mai kira ga Najeriya ta haɗa kai da Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.