Mutum 9 Sun Mutu, fiye da 20 Sun Samu Raunuka a Turmutsutsun Nema Aikin Soja a Ghana
- Mutane akalla shida sun mutu sakamakon cunkoson matasa da aka samu a wajen daukar sojoji a babban birnin Ghana
- Rundunar sojin Ghana ta ce mutane 22 sun ji rauni, yayin da gwamnatin kasar ta dakatar da daukar sababbin sojoji
- Shugaba John Mahama ya ziyarci asibitin sojoji, inda dangi da iyalai suka cika suna kuka da neman labarin ‘yan uwansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ghana - An samu tashin hankali a kasar Ghana a ranar Laraba yayin da akalla mutane shida suka mutu a cunkoson masu neman aikin soja.
An rahoto cewa an yi turmutsun ne a yayin shirin daukar sojoji da aka gudanar a filin wasan El-Wak Sports Stadium da ke Accra, babban birnin kasar.

Source: Twitter
Mutum 6 sun mutu a cunkuson shiga soja
A cewar rundunar sojin kasar, lamarin ya faru ne lokacin da taron matasa masu neman aiki suka ture ƙofofin filin wasan domin shiga kafin a fara tantance su, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa, rundunar sojin Ghana ta tabbatar da cewa “mutane shida sun rasa rayukansu”, yayin da mutane 22 suka ji rauni, inda biyar suke cikin mawuyacin hali.
Hukumar lafiya ta sojoji ta bayyana cewa wadanda suka ji rauni suna karbar magani a asibitin sojoji na 37 da ke Accra.
Haka kuma, a birnin Kumasi, wasu mutane biyar sun ji rauni a irin wannan cunkoso yayin wani shirin daukar aiki da aka gudanar a yankin Kudancin kasar.
Gwamnati ta dakatar da daukar sabbin sojoji
A cikin wata sanarwa ta biyu da rundunar sojin ta fitar daga baya a shafinta na X, gwamnatin kasar ta yanke shawarar dakatar da shirin daukar sababbin sojoji.
Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa rundunar tsaron kasar ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin faruwar wannan mummunan lamari.
An ce cunkoson ya faru da misalin karfe 6:20 na safe, lokacin da matasa suka karya shingayen tsaro da ake amfani da su wajen shigar da masu nema.
A asibitin sojoji na 37 da ke Accra, an samu yanayi mai cike da tashin hankali da kuka, yayin da iyalai suka taru suna neman labarin ‘yan uwansu.
Wasu suna riƙe da wayoyi da katin shaida, yayin da ma’aikatan lafiya ke kokarin ceto rayuka a dakin ba da agajin gaggawa.

Source: Twitter
Shugaban Ghana ya ziyarci asibitin sojoji
Shugaban kasar Ghana, John Mahama, ya isa asibitin karkashin tsaro mai tsauri domin duba wadanda suka ji rauni, yayin da ya bi daki bayan daki.
Yayin ziyarar, ya bayyana cewa lamarin abin takaici ne, inda rundunar tsaro ta kasar, a sanarwar da ta fitar a shafinta na intanet, ta ruwaito Mahama ya tattauna da wadanda suka jikkata.
Shugaba Mahama ya samu rakiyar mukaddashin ministan tsaro, Dr. Cassiel Ato Forson, mataimakin ministan tsaro, Hon Ernest Brogya Genfi da hafsan tsaron kasa, Laftanal Janar William Agyapong.
Congo: Mutane sun mutu wajen neman shiga soja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matasa 37 sun bakunci lahira sakamakon wani turmutsutsu da ya barke a filin wasa na Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo.
Matasan sun je filin ne domin a tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama.
Yayin da ake jiran samun cikakkun bayanai kan yadda lamura suka faru a wajen ba, Firayim Minista Anatole Collinet Makosso ya kira lamarin "mummunan iftila'i".
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


