Kotu Ta Bada Belin Tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, Ya Fito bayan Mako 3 a Kurkuku

Kotu Ta Bada Belin Tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, Ya Fito bayan Mako 3 a Kurkuku

  • Kotun Faransa ta saki tsohon shugaban ƙasa Nicolas Sarkozy bayan ya shafe mako uku kacal a gidan yari daga cikin daurin shekaru biyar
  • An sanya wa Sarkozy ƙa’idoji masu tsauri bayan sakin sa, ciki har da hana shi barin ƙasa a shari’ar kuɗin Mu'ammar Gaddafi da ake yi da shi
  • Da yake magana bayan fitowa daga gidan yari, Sarkozy ya ce ba zai taɓa amincewa da laifin da bai aikata ba, kuma gaskiya za ta yi halinta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Paris, France – Tsohon shugaban ƙasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya samu ’yanci daga gidan yari bayan ya shafe mako uku kacal daga cikin hukuncin shekaru biyar da aka yanke masa.

An yanke masa hukuncin ne saboda zargin karbar wasu kudi da ya y kamfen da su a zaben 2007 daga marigayi shugaba Muammar Gaddafi na kasar Libiya.

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu

Kotu ta bada belin Sarkozy
Tsohon Shugaban kasar Faransa Hoto: @IGIHE
Source: Twitter

BBC ta wallafa cewa kotun Faransa ta bada belinsa ne a ƙarƙashin kulawar shari’a mai tsauri, tare da hana shi barin ƙasar kafin fara daukaka kara da ya yi da ake sa ran gudanarwa a farkon shekarar 2026.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Sakorzy bayan barin fursun

Aljazeera ta ruwaito cewa bayan fitowarsa daga gidan yari La Santé da ke Paris, Sarkozy ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa:

“Ƙarfina yanzu gaba ɗaya yana kan tabbatar da gaskiyata. Gaskiya za ta yi nasara… labarin bai ƙare ba.”

An ruwaito motar tsohon Shugaban ta bar gidan yarin da misalin 3.00 na rana agogon Paris, kuma daga bisani an hango shi ya isa gidansa da ke yammacin birnin.

Sharuɗɗan belin Sarkozy

Ɗaya daga cikin sharuɗɗan belin shi ne cewa Sarkozy ba zai tuntubi wasu shaidu ko ma’aikatan ma’aikatar shari’a da ke da alaƙa da shari’ar ba.

An saki Sarkozy bayan mako 3 a daure
Tsohon shugaban Faransa, Sarkozy da ake zargi da karbar cin hanci Hoto: @IGIHE
Source: Twitter

Ɗaya daga cikin lauyoyinsa, Christophe Ingrain, ya bayyana belin a matsayin ci gaba, yana mai cewa tawagar su za ta mai da hankali kan shirin shari’ar da za ayi a watan Maris mai zuwa.

Kara karanta wannan

Mexico: Wani Mutum ya taba nonon shugabar kasa, ya yi kokarin sumbatarta a taro

A lokacin da yake a gidan yari, ministan shari’a Gérald Darmanin ya kai masa ziyara – abin da ya jawo ƙorafe-ƙorafe daga jama'a.

Lauyoyi 30 sun yi korafi, waɗanda suka ce hakan na iya jawo rikici saboda Darmanin tsohon abokinsa ne.

A lokacin da ya bayyana a gaban kotu ta hanyar bidiyo, Sarkozy ya ce zama a keɓe shi kaɗai a gidan yari ya kasance mai tsanani da firgici.

Ya ce:

“Ban taɓa yin tunanin neman kuɗi daga Gaddafi ba. Ba zan taɓa amincewa da abin da ban aikata ba."

Ya kuma yaba da tausayin ma’aikatan gidan yari da suka taimaka wajen sauƙaƙa masa lokacin da ya shafe a ciki.

Matarsa, Carla Bruni-Sarkozy, da ’ya’yansa biyu – Jean da Pierre – sun halarci zaman kotun don nuna goyon baya ga mahaifinsu.

Kotu Faransa ta yanke wa Sarkozy hukunci

A baya, mun ruwaito cewa wata kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari kan tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy bisa zargin karbar cin hanci daga Mu'ammar Gaddafi.

Sarkozy ya zama shugaban kasa na farko daga wata kasar Tarayyar Turai (EU) da aka daure a gidan yari, a yayin da ya ke kara karyata zargin da ake yi masa a lokacin yana neman zabe.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Trump, gwamnatin Najeriya ta yi magana kan shari'ar 'yan ta'adda

Kotu ta samu Sarkozy, wanda ya jagoranci Faransa daga 2007 zuwa 2012, da laifin karbar haramtaccen kudin kamfen daga tsohon shugaban Libya, Marigayi Muammar Gaddafi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng