Kisan Kiristoci: Kasar Rasha Ta Tsoma Baki kan Shirin Amurka na Kai Farmaki Najeriya

Kisan Kiristoci: Kasar Rasha Ta Tsoma Baki kan Shirin Amurka na Kai Farmaki Najeriya

  • Gwamnatin kasar Rasha ta ce tana bin diddigin halin da Najeriya ke ciki bayan Amurka ta yi barazanar kai mata farmaki
  • Ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta gargadi Amurka cewa ya zama dole ta bi dokokin kasa da kasa wajen daukar kowane irin mataki
  • Hakan dai na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi, lamarin da Najeriya ta musanta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Russia - A karon farko, kasar Rasha ta tsoma baki kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na kawo farmaki Najeriya.

Trump dai ya yi barazanar cewa da yiwuwar ya bai wa sojojin Amurka umarnin kawo farmaki wasu sassan Najeriya domin kakkabe yan ta'adda da ke yiwa kiristoci kisan kiyashi.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Shugaba Trump, Putin da Bola Tinubu.
Hoton Shugaba Donald Trump, Shugaba Vladimir Putin da Bola Ahmed Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Rasha ta yi magana

TRT World ta tattaro cewa gwamnatin Rasha ta ce tana bin diddigin rahotanni da ke cewa Amurka na shirin kai farmaki a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rasha ta gargadi Amurka cewa duk wani mataki da za a ɗauka dole ne ya kasance bisa ka’idodin doka ta ƙasa da ƙasa.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ce ta bayyana haka a ranar Juma’a yayin taron manema labarai a Moscow.

“Muna lura da sa ido sosai da wannan batu, kuma muna kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su bi ƙa’idodin doka ta ƙasa da ƙasa yadda ya kamata,” in ji Zakharova.

Wace barazana Trump ya yi wa Najeriya?

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Hakan ya zo ne bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, inda ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka ta fara shirin kai farmaki Najeriya.

A cewar Trump, ya umarci ma'aikatar da ta tsara yiwuwar daukar matakin soji don kare rayukan Kiristoci a Najeriya.

Duk da cewa babu wata tabbaci a hukumance daga Washington kan wannan shiri, kalaman Trump sun jawo hankalin ƙasashe da dama, ciki har da Rasha.

A martanin da ta mayar, kasar Rasha ta jaddada cewa duk wani mataki da za a ɗauka ya girmama ikon ƙasashe da tsarin doka ta duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Honon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Najeriya ta musanta zargin Trump

Najeriya dai ta ƙaryata zargin Amurka cewa ana zaluntar Kiristoci a ƙasar, tana mai cewa babu wani tsarin gwamnati da ke nuna bambanci a addini.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya

A wannan makon, Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya yi gargadi kan duk wani ƙoƙari na tayar da hankula ko kawo rabuwar kai a Najeriya.

Rasha dai ta dade tana adawa da tsoma bakin da Amurka ke yi a harkokin cikin gida na ƙasashe masu tasowa, tana jaddada manufarta ta mutunta ‘yancin kowace ƙasa wajen tafiyar da lamuranta.

Manufar shirin Amurka kan Najeriya

A baya, mun kawo muku cewa Farfesa Lai Olurode ya bayyana cewa ko kadan ba don kare rayukan kiristoci Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kawo farmaki Najeriya ba.

Tsohon malami a jami'ar UNILAG ya bukaci manyan Najeriya su hada kai wajen kare kasarsu daga masu tsoma baki daga ketare.

Farfesan ya kuma danganta matsayar Trump da rashin jin daɗin Amurka kan ci gaban masana’antar mai a Najeriya, musamman bayan bude matatar mai ta Dangote.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262