Kotu Ta Raba Gardama da Yaro Ya Kai Karan Iyayensa kan Kawo Shi Makaranta a Afirka

Kotu Ta Raba Gardama da Yaro Ya Kai Karan Iyayensa kan Kawo Shi Makaranta a Afirka

  • An kammala zaman shari'a kan karar da yaro dan shekara 14 ya kai iyayensa kotu saboda sun kai shi makarantar kwana a Ghana
  • Rahoto ya nuna cewa iyayen yaron, wadanda ke zaune a birnin Landan na kasar Ingila sun yi haka saboda ganin dansu na neman lalacewa
  • Kotu ta umarci yaron ya ci gaba da zama a Ghana har zuwa lokacin da zai kammala jarabawa rGCSE, sannan ya koma Ingila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

England - Kotun Ingila ta yanke hukunci a karar da wani yaro ɗan shekara 14 ya kai iyayensa saboda sun dauke shi daga birnin Landan, sun tura shi makarantar kwana a Afirka.

Kara karanta wannan

Mexico: Wani Mutum ya taba nonon shugabar kasa, ya yi kokarin sumbatarta a taro

Kotun ta yanke hukuncin cewa yaron da ya shigar da karar zai ci gaba da zama a kasar Ghana har sai ya kammala jarabawar GCSEs.

Kotu.
Hoton gudamar kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC News ta ruwaito cewa iyayen yaron, wanda ba a bayyana sunansa ba saboda dalilan shari’a, sun tafi da shi zuwa Ghana a watan Maris 2024 da nufin gaida wani dan uwansu da bai da lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin dauko yaron daga Ingila zuwa Ghana

Iyayensa sun yi hakan ne saboda damuwar da suke da ita game da halayyarsa a Landan, ciki har da kin zuwa makaranta, rashin sanin inda yake samun kudi, da kuma zargin ɗaukar wuƙa.

Yaron dai ya musanta cewa yana cikin wata kungiya ko yana ɗaukar makami.

A hukuncin da aka yanke ranar Litinin, alkalin kotun, Misis Justice Theis, ta ce yaron ya ci gaba da zama a Ghana har sai ya kammala karatunsa na GCSE.

A cewarta, komawarsa Ingila yanzu “zai iya haifar masa da matsala da koma baya a harkar neman ilimi da ta zamantakewa.”

Yadda yaron ya maka iyayensa a kotu

Kara karanta wannan

Bayan daura aure, matashi 'dan shekara 25 ya caka wa matarsa wuka har lahira a Sakkwato

Tun a watan Fabrairu, yaron ya koka cewa yana cikin “wata irin azaba” a Ghana, yana jin baƙin ciki, kadaici, da kuma rashin fahimtar al’adar kasar.

Ya bayyana cewa baya jin harshen Twi, yana daukar kansa kamar baƙo, kuma yana da matsalar samun abokai.

Lauyansa James Netto, ya ce wannan lamari “mai matuƙar wahala ne a kowane mataki,” yana mai cewa yaron “bai taɓa tunanin kai iyayensa kotu ba, amma ba shi da wani zaɓi tunda sun ɗauki matakin da bai yarda da shi ba.”

Kotun Ingila ta yanke hukunci

Alkalin ta ƙara da cewa:

“Na sani cewa wannan hukunci bai yi daidai da muradin yaron ba, amma ina ganin hakan ne zai fi amfani gare shi da iyalinsa. Yana da basira, hankali da damar da za su taimaka masa ya ci gaba da karatu cikin nasara.”

Kotun ta bayyana cewa za a tsara jadawalin dawowarsa Ingila bayan kammala GCSEs, ciki har da shiga horon sulhu da iyali, cewar rahoton Ghana Web.

Dalibai a makaranta.
Hoton dalibai su na daukar darasi a makaranta Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, ta nuna cewa za a sake duba lamarin idan lokacin komawa Ingila ya yi, domin tabbatar da cewa yaron ya shirya komawa gida cikin kwanciyar hankali da haɗin kai da iyalinsa.

Kara karanta wannan

TUC: Yan kwadago sun taso Gwamnatin Tinubu kan shirin kakaba harajin 15% kan fetur

Kotun Ingila ta daure dan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a Ingila ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Lucius Njoku hukuncin zaman gidan yari na tsawon makonni 16.

Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan kama Njoku da laifin amfani da bayanan karya wajen aiki a asibitin lardin Cheshire, ƙasar Ingila.

An gano cewa a tsakanin Fabrairu zuwa Afrilu 2024, Njoku ya yi aiki a sashen gaggawa (A&E) na asibitin da sunan wata kawarsa ‘yar Najeriya mai suna Joyce George.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262