Mexico: Wani Mutum Ya Taba Nonon Shugabar Kasa, Ya Yi Kokarin Sumbatarta a Taro

Mexico: Wani Mutum Ya Taba Nonon Shugabar Kasa, Ya Yi Kokarin Sumbatarta a Taro

  • Wani mutum ya shiga hannun yan sandan Mexico bayan kokarin taba maman shugabar kasar mai shekaru 63
  • An kama mutumin ne da ya yi wa shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, wani ɗanyen aiki ta hanyar rungumar ta
  • Shugabar kasar ta bayyana cewa za ta dauki mummunan mataki kan haka domin dakile cin zarafin mata da ake fuskanta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Mexico - Shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta ce za ta gurfanar da wani mutum da ya yi kokarin cin zarafinta.

Shugaba Sheinbaum ta kasar Mexico ta nuna damuwa kan abin da ya faru na cin zarafi yayin wata ganawa da jama’a a Mexico City.

Shugabar kasar za ta ɗauki mataki da wani ya ci mata zarafi
Shugabar kasar Mexico, Claudia Sheinbaum yayin taro. Hoto: Claudia Sheinbaum Pardo.
Source: Facebook

An ci zarafin shugabar kasar Mexico

Bidiyon da aka ɗauka da wayar salula ya nuna mutumin yana zuwa bayanta ya yi ƙoƙarin sumbatarta a wuya tare da taɓa jikinta kafin ta matsa gefe, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Dalilin Peter Obi na zagaya Najeriya, ya na ba makarantu kyautar miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin tawagarta ya shiga tsakani cikin gaggawa, inda aka kama mutumin nan take, yayin da Sheinbaum ta nuna damuwa sosai da abin da ya faru.

An ce mutumin ya taba mamanta ta baya har da kuma kokarin sumbatarta saboda wasu dalilai na shi na karan kansa.

Ta ce:

“Idan ban kai ƙara ba, me zai faru da sauran mata? Idan sun yi wa shugabar ƙasa haka, me zai faru da saura?”

Sheinbaum ta ce ta yanke shawarar kai ƙarar ne saboda wannan ba sabon abu ba ne ga mata a ƙasar, inda ta ce ta fuskanci haka tun tana ɗaliba.

Ta kuma bayyana cewa wanda ake zargi ya taba cin zarafin mata a cikin taro, saboda haka “dole ne a ja layi” wajen hana irin wannan aiki.

Wani ya ci zarafin shugabar Mexico a taro
Shugaba Claudia Sheinbaum kenan yayin taro a Mexico. Hoto: Claudia Sheinbaum Pardo.
Source: Facebook

Abin da kungiyoyin kare hakkin mata suka ce

Kungiyoyin kare haƙƙin mata sun ce lamarin ya nuna yadda al’adar zaluntar mata ke daɗa ƙaruwa a Mexico, inda mata ke fuskantar cin zarafi da rashin kariya.

Kara karanta wannan

TUC: Yan kwadago sun taso Gwamnatin Tinubu kan shirin kakaba harajin 15% kan fetur

Lamarin ya kuma sake tayar da maganar tsaron shugabanni a ƙasar, musamman ganin yadda shugabar ke son hulɗa kai tsaye da jama’a a tituna.

CNN ta ruwaito Sheinbaum na cewa duk da abin da ya faru, ba za ta daina haduwa da magoya bayanta kai tsaye ba, saboda tana son ci gaba da kusanci da su.

Hakan na zuwa ne bayan kisan basaraken Uruapan, Carlos Manzo, wanda aka kashe yayin bukukuwan 'Day of the Dead', bayan ya roƙi ƙarin kariya daga gwamnati.

An tuna cewa Sheinbaum ta fara aiki da tsaurara tsaro da yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi, musamman fentanyl.

An naushi shugaban majalisa a Mexico

A baya an ji cewa rigima ta barke tsakanin sanatoci a Majalisar Dattawan Mexico yayin da aka zargi yan jam'iyyun adawa da cin amanar kasa.

Rahoto ya nuna cewa rikicin ya kai ga doke-doke tsakanin sanatocin jam'iyyun adawa da mai mulki.

Shugaban Majalisar Dattawan Mexico ya yi barazanar kai kara kotu kan dukan da sanatan jam'iyyar adawa ya yi masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.