'Yan Majalisar Amurka Sun Taso Miyetti Allah a gaba kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

'Yan Majalisar Amurka Sun Taso Miyetti Allah a gaba kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

  • Majalisar Dokokin Amurka ta fra daukar matakai da ke nuna goyon bayan ga Shugaban kasar, Donald J Trump bayan kalamansa a kan Najeriya
  • Donald Trump ya yi zargin cewa ana yiwa kiristocin Najeriya kisan kare dangi, saboda haka kasarsa ba za ta zuba ido a cigaba da hakan ba
  • Trump ya fara da daukar matakin sanya Najeriya a matsayin kasashen da ake samun damuwa a kansu a kan kisan kiyashin Kiristoci a duniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Majalisar Wakilan Amurka ta bukaci Ma’aikatar harkokin waje da ma’aikatar kudin kasar da su kakaba takunkumi kan wasu mutane da kungiyoyi a Najeriya.

Daga cikin wadanda ta bukaci a dauki wannan mataki a kansu akwai kungiyar makiyaya ta MACBAN da Miyetti Allah Kautal Horê.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

'Yan majalisar Amurka sun nemi a saanya wa Miyetti Allah takunkumi
Shugaban Amurka, Donald Trump, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Donald J Trump/@PBAT
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa 'yan majalisa sun mika bukatar ne saboda zargin take hakkin addini a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisar Amurka sun durfafi Miyetti Allah

The Street Journal ta wallafa cewa wannan bukata na kunshe a cikin wani kudiri da aka gabatar a gaban Majalisar ranar Talata.

An gabatar a matsayin H. Res. 860 a zaman Majalisar 119, wanda 'dan majalisa Christopher Smith ya gabatar da takwaransa, Paul Huizenga.

Smith ya kara da yaba wa Donald Trump a kan yadda ya hango dacewar ya yi wa kasa mai cin gashin kanta barazana da yaki.

Trump ya nace a kan ana kashe kiristoci a Najeriya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

A karshen mako, Shugaba Donald Trump ya bayyana Najeriya a matsayin kasa da ake kisan kiristoci ba ji, ba gani.

Shugaban ya kuma ya yi barazanar daukar matakin soji idan kasar ba ta dakatar da zargin kisan Kiristoci ba kuma ta ba ta hadin kai wajen hakan ba.

Dalilin daukar matakin 'yan majalisar Amurkan

Kara karanta wannan

'Da gaske ne ana kisan kiyashi a Najeriya,' Jigon APC ya goyi bayan Donald Trump

Masu gabatar da kudirin sun nuna damuwa kan zargin yadda ake ci gaba da zaluntar Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya.

Sun kawo jerin rahotanni daga kafofin yaa labarai da kungiyoyin farar hula, suna zargin manyan hare-hare kan fararen hula, lalata wuraren ibada, da kuma rashin hukunci ga masu laifi.

Kudirin ya ce:

“Tsawon shekaru fiye da 10, kungiyoyin masu tayar da tarzoma na Musulunci suna kiashe mutane, satar mutane da sauran manyan laifuffuka, galibi kan Kiristoci da musulmai masu sassaucin ra'ayi, wanda hakan ya haifar da keta hakkin mutane da rushe wuraren ibada.”

Haka kuma, an bayyana cewa an tsangwami manyan shugabannin addini, kamar su Father Remigius Iyhula da Bishop Wilfred Anagbe, kan bayaninsa a kan kisan kiristoci.

Kudirin ya bayar da shawarar cewa a dakatar da taimakon kasashen waje na Amurka har sai Najeriya ta dauki matakin kare hakkin addini da hukunta masu laifi.

An kuma bukaci Amurka ta kakaba takunkumi, ciki har da hana biza da daskare kadarori bisa tsarin Global Magnitsky, ga Miyetti Allah da sauran kungiyoyin da ake zargi da take hakkin addini a jihar Binuwai da Filato.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya

Martanin Miyetti Allah ga gwamnatin Amurka

Abdullahi Bakoji Adamu, Shugaban Miyetti Allah na jihar Kano ya shaida wa Legit takaicin matakin da Amurka ke shirin dauka ba.

Ya ce bai kamata Amurka ta ɗauki mataki bisa zargin da ba a gudanar da cikakken bincike a kansa ba.

Bakoji, wanda shi Darakta ne na ƙasa na hukumar kare hakkin ɗan adam ga IHRC-RFT) reshen Najeriya, ya ce ba adalci ba ne a ɗora wa ƙungiya alhakin abin da wasu ‘yan kaɗan suka aikata.

A Kalamansa:

“Abu ne mai haɗari a ɗauki irin waɗannan matakai ba tare da cikakken bincike ba."
"Idan mutum ɗaya ne ya karya doka, to shi ne ya kamata a bincika kuma a hukunta, ba duka ƙungiyar ba.”

Sakon Tinubu bayan barazanar Amurka

A baya, mun wallafa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya da su kwantar da hankulansu duk da barazanar Amurka a kan kasar nan na kawo hari.

Kara karanta wannan

Trump ya kara nuna yatsa ga Najeriya, ya ce ba za a ji da dadi ba

Tinubu ya lallashi jama'a ne ta bakin Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris bayan an fara zaman dar-dar a kan bazanar da Donald Trump ya yi.

Shugaban kasan ya ce ana bibiyar dukkanin bayanan da Amurka ta yi, ana nazarinsu sannan za a dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da kare rayukan 'yan kasa daga ta'addanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng