Halin da Ake Ciki a Guinea Bissau bayan Yunkurin Juyin Mulki

Halin da Ake Ciki a Guinea Bissau bayan Yunkurin Juyin Mulki

  • Ana zargin cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin farar hula a kasar Guinea-Bissau da ke yankin Afirka ta Yamma
  • Sojoji sun samu nasarar cafke wasu manyan jami'ai da ake zargin akwai hannunsu a yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Embalo
  • Yunkurin juyin mulkin dai na zuwa ne yayin da ake fara shirin gudanar da kamfen domin zaben shugaban kasa da ke tafe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Guinea-Bissau - Sojojin Guinea-Bissau sun ce sun hana yunkurin juyin mulki da nufin tayar da tarzoma a kasar.

Hakazalika sun kama manyan jami’an sojoji da ake zargi da kokarin rushe tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar.

An so kifar da gwamnatin Umaro Embalo a Guinea-Bissau
Shugaba Umaro Embalo da sojoji suka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa Hoto: @USEmbalo
Source: Twitter

Wannan sanarwar, wacce tashar TRT Afrika ta ruwaito, ta zo ne kwana ɗaya kafin fara yakin neman zaben majalisa da na shugaban kasa, wanda aka shirya farawa a yau Asabar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi yunkurin juyin mulki a Guinea-Bissau

Mataimakin babban hafsan sojin kasar, Janar Mamadu Ture, yayin wani taron manema labarai a Bissau ranar Jumma’a, ya bayyana cewa yunkurin juyin mulkin na da nufin hana gudanar da zabe.

Sai dai ya ki bayyana adadin jami’an da aka kama ko cikakkun bayanai game da yadda aka tsara yunkurin juyin mulkin, rahoton tashar Aljazeera ya tabbatar da labarin.

An tattaro cewa, cikin waɗanda aka kama har da Brigediya Janar Daba Nawalna, shugaban cibiyar horar da sojoji da ke kimanin kilomita 30 daga babban birnin kasar, Bissau.

Shugaba Embalo ya yi gargadi

Shugaba Umaro Embaló, wanda ke neman wa’adin mulki na biyu, a ranar Alhamis ya yi gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da wata tarzoma ba a lokacin kamfen.

“Ba za mu lamunci tashin hankali ba. Gwamnati ta ɗauki duk matakan da suka dace don kare lafiyar kowanne ɗan takara a lokacin wannan kamfen."

Kara karanta wannan

An 'gano' sojan da aka tura ya hallaka Ribadu a zargin yunkurin juyin mulki

- Umaro Embalo

Kamen jami’an ya zo a lokacin da ake shirin zaben shugaban kasa a kasar ta yankin Afirka ta Yamma, wanda ake hasashen zai kasance mai rinjaye ga Embaló bayan da aka hana babbar jam’iyyar adawa shiga zaben.

Guinea-Bissau ta sha fama da rikicin siyasa da juyin mulki tun bayan samun ’yancin kai daga kasar Portugal a 1974.

Amma tun bayan zaben shugaban kasa na 2014, kasar ta fara kokarin tabbatar da dimokuraɗiyya da doka.

Wannan sabon lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.

An yi yunkurin juyin mulki a Guinea-Bissau
Shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Embalo Hoto: @USEmbalo
Source: Twitter

Ana juyin mulki a kasashen Afrika

Tun daga shekarar 2020, kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, da Guinea duk sun fuskanci juyin mulki da ya kifar da gwamnatocin da aka zaba ta dimokuraɗiyya.

Ko da yake ta kasance cikin natsuwa a ’yan shekarun nan, Guinea-Bissau na daga cikin ƙasashen da suka fi samun rikice-rikice a yankin Afrika ta Yamma.

Kara karanta wannan

Ajali ya gitta: Saurayi ya mutu daga zuwa zance wurin budurwa a jihar Yobe

Kasar ta fuskanci fiye da yunkurin juyin mulki guda 10, inda sojoji ke da tasiri sosai a harkokin siyasa.

A shekarar 2022, an kai hari kan fadar shugaban kasa, wanda Embaló ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Batun yunkurin juyin mulki a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu bayanai kan dakarun sojojin da ake zargin sun shirya gudanar da juyin mulki a Najeriya.

Majiyoyi sun bayyana cewa daga cikin jami’an 16 da ake tsare da su, 14 sojojin ƙasa ne, sai kuma sojan ruwa daya da kuma sojan sama daya.

Hakazalika, majiyoyin sun tabbatar da cewa tabbatar da cewa 15 daga cikin sojojin da ake tsare da su sun fito ne daga yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng