Samia Suluhu: Mace Ta Lashe zaben Shugaban Kasar Tanzania

Samia Suluhu: Mace Ta Lashe zaben Shugaban Kasar Tanzania

  • An bayyana shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan a matsayin wacce ta lashe zaben shugaban ƙasa
  • Zaben ya haifar da tashin hankali da zanga-zanga a manyan birane bayan hana manyan ’yan adawa tsayawa takara
  • Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan rahotannin mutuwar mutane da dama yayin tarzomar bayan zabe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tanzania - An bayyana shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a matsayin wacca ta sake lashe zaben shugaban ƙasa da kusan kashi 98 na ƙuri’un da aka kada,.

Samia Suluhu Hassan ta yi nasara ne duk da koke-koken da ke cewa an hana manyan ’yan adawa shiga zaben.

Samia Suluhu Hassan
Shugabar Tanzania da ta lashe zabe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce hukumar zaɓe ta ƙasa ce ta tabbatar da sakamakon a ranar Asabar, inda ta ce Hassan ta samu nasara a kusan dukkan mazabu na ƙasar.

Kara karanta wannan

Trump ya sa Najeriya a jan layi kan zargin kashe Kiristoci, Amurka za ta yi bincike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a rantsar da shugabar Tanzania

Rahotanni daga kafafen labaran gwamnati sun ce an shirya bikin rantsar da shugabar a yau Asabar, jim kaɗan bayan sanar da sakamakon.

BBC ta rahoto cewa zaben ya tayar da tarzoma a wasu sassa na ƙasar, inda masu zanga-zanga suka fito suna nuna adawa da abin da suka kira “zaben danniya da wariya.”

Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan
Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan tana wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An ruwaito cewa a ranar zabe, duk da tsauraran matakan tsaro, an yi arangama tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zanga, aka yi amfani da borkonon tsohuwa da harbin bindiga.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ƙone gine-ginen gwamnati da kuma jefa ƙasƙantattun kalmomi ga hotunan shugabar kasar.

Mutane sun mutu rikicin zaben Tanzania

Jam’iyyar adawa ta Chadema, wadda aka hana shiga zaben, ta yi ikirarin cewa fiye da mutane 700 ne suka rasa rayukansu, bisa bayanan da ta tattara daga asibitoci da cibiyoyin lafiya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

Sai dai ofishin kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 a birane uku.

Ministan harkokin wajen ƙasar, Mahmoud Thabit Kombo, ya shaida cewa gwamnati ta gudanar da zaben cikin adalci kuma ba ta yi amfani da ƙarfi fiye da kima ba.

Mahmoud Thabit Kombo ya ƙara da cewa babu wata hujja ta mutuwar mutane ɗaruruwan kamar yadda aka ruwaito.

Kiran majalisar dinkin duniya ga gwamnatin Tanzania

Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana “babbar damuwarsa” kan halin da ake ciki a Tanzaniya.

Ya koka kan abubuwan da suka faru, musamman kan mace-mace da raunata mutane yayin zanga-zanga, ya bukaci gwamnati ta kare rayukan jama’a da ta gudanar da bincike kan abin da ya faru.

Paul Biya ya lashe zaben Kamaru

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya lashe zabe bayan fafatawa da manyan 'yan adawa.

Legit Hausa ta gano cewa an sanar da Paul Biya ne bayan shafe mako biyu ana kirga kuri'un da 'yan kasar suka kada.

Kara karanta wannan

'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda

Babban jagoran 'yan adawa na kasar da ya fafata da Paul Biya, Issa Bakary ya ki yarda da sakamakon zaben da aka sanar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng