Trump Ya Sa Najeriya a Jan Layi kan Zargin Kashe Kiristoci, Amurka za Ta Yi Bincike
- Donald Trump ya yi magana kan zargin cewa ana kashe Kiristoci duk da gwamnatin Najeriya ta ce ba haka ba ne
- Ya ce dubban Kiristoci na mutuwa a hannun ’yan ta’adda, yana kiran majalisar dokokin Amurka ta binciki lamarin
- Wannan mataki ya dawo da tsohuwar takaddama da aka samu tun a 2020 lokacin mulkin Donald Trump na farko
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya a matsayin kasar da zai sakawa ido (CPC) bisa zargin ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi.
Wannan matakin na zuwa ne bayan watanni uku da gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin biza ga ’yan Najeriya, inda aka takaita izinin shiga ƙasar daga Abuja.

Source: Facebook
Trump ya bayyana wannan matakin ne a ranar Juma’a ta hanyar sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, wanda kuma aka yada a shafin White House na X.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi wa Trump martani mai zafi kan zargin kashe Kiristoci, ta ce karya ne
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya ce a binciki Najeriya
Shugaban Amurka ya umurci mambobin majalisar dokoki, Riley Moore da Tom Cole, su gudanar da cikakken bincike kan rahotannin kisan Kiristoci a Najeriya tare da gabatar masa da sakamako.
Ya ce:
“Amurka ba za ta tsaya gefe tana kallo ba yayin da irin waɗannan mummunan laifuffuka ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe. Za mu dauki mataki don kare Kiristoci a duniya.”
Wannan umarni ya sake tayar da tsohon ce-ce-ku-ce wanda ya tashi tun a watan Disamba 2020 lokacin da Trump a wa’adinsa na farko.

Source: Facebook
Rahoton Hudson Institute ya ce a karkashin Muhammadu Buhari, Trump ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke karkashin CPC.
Daga baya, gwamnatin Joe Biden ta cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen a cikin watan Nuwamba 2021.
Tsohon ministan harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce duk da matsalolin tsaro, ba a samu hujja cewa gwamnatin Najeriya na da hannu kai tsaye a take ’yancin addini ba.

Kara karanta wannan
'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda
Me matakin Trump ke nufi ga Najeriya?
A cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ƙasashen da ake sanyawa cikin jerin wadanda ake saka wa ido (CPC) su ne waɗanda ke halarta ko take ’yancin addini.
Ma'aikatar ta lissafa laifuffuka kamar tsarewa na dogon lokaci, azabtarwa, salwantar da ran mutum ko kisa saboda addini cikin abubuwan da za su saka a dauki matakin.
Matakin na bai wa shugaban Amurka damar ɗaukar matakai kamar takunkumi, rage hulɗar diflomasiyya ko cire tallafi, gwargwadon la’akari da bukatun ɗan Adam ko tsaron ƙasa.
A halin yanzu, ƙasashen da suka haɗa da China, Iran, Rasha, Koriya ta Arewa, Saudiyya da Eritrea suna cikin wannan jerin kasashen da Amurka ta sanya karkashin CPC.
Sultan ya karyata zargin kisan Kiristoci
A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi na Najeriya ya karyata zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Legit Hausa ta gano cewa Sarkin Musulmi ya yi magana ne karkashin majalisar kolin addinin Musulunci ta Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan wasu daga cikin Sanatocin Amurka sun yi magana kan zargin da wani mutum ya yi kan batun.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
