'Dan Najeriya Ya Yi Amfani da Kayan Aikin Mace, Ya Burma Kansa a Matsala a Ingila

'Dan Najeriya Ya Yi Amfani da Kayan Aikin Mace, Ya Burma Kansa a Matsala a Ingila

  • Wani 'dan Najeriya, Lucius Njoku ya jefa kansa a matsala bayan ya yi amfani da sunan wata kawarsa ma'aikaciyar jinya a kasar Ingila
  • Kotun Ingila ta kama shi da laifin amfani da bayanan mace tare da yin aiki a matsayin ma'aikacin jinya, lamarin da ya saba wa doka
  • Mai Shari'a John McGarva ya yanke wa Njoku hukuncin daurin watanni 16 a gidan yari tare da tarar fan 239 kusan Naira raba miliyan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Chester, Ingila – Wata kotu da ke Chester a kasar Ingila ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Lucius Njoku hukuncin zaman gidan yari na tsawon makonni 16.

Kotun ta daure mutumin ne bayan ta same shi da laifin sojan gona a matsayin ma'aikaciyar jinya mace a Asibitin Countess of Chester da ke lardin Cheshire, ƙasar Ingila.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

Kotun Ingila.
Hoton gudumar kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wane laifi dan Najeriya ya yi a Ingila?

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a tsakanin Fabrairu zuwa Afrilu 2024, Njoku ya yi aiki a sashen gaggawa (A&E) na asibitin da sunan wata kawarsa ‘yar Najeriya mai suna Joyce George, wadda ke zaune a garin Ellesmere Port.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin gwamnati sun ce George, ma'aikaciyar jinya ce watau nas mai rajista a karkashin wani kamfani.

Bayanai sun nuna cewa ta ba abokinta dan Najeriya, Njoku damar yin amfani da sunanta da takardunta wajen zuwa aiki maimakon ta.

Asibitin sun tsorata da danyen aikin

A lokacin da lamarin ya faru, Njoku ya kasance yana taimakawa wajen kula da marasa lafiya, yana musu wanka, kuma ya saka musu kaya tare da duba lafiyarsu.

Lauyar gwamnati, Lisa McGuire ta ce wannan lamari ya haifar da babban damuwa game da tsaro da tsarin shiga asibitin.

“An yi sa’a babu wanda ya ji rauni ko ya koka game da aikinsa, amma matsalar ita ce yadda ya samu damar shiga asibitin cikin sauƙi.”

Kara karanta wannan

"Yara sama da 100,000 na cikin barazana": Manyan Arewa sun waiwayi almajirai

Yadda aka kama dan Najeriya da laifi

Jami’an bincike sun gano cuwa-cuwan ne bayan ’yan sanda sun kai samame gidan Joyce George, inda suka samu saƙonnin waya tsakaninta da Njoku suna tattaunawa kan jadawalin aiki.

An ruwaito cewa George ta tsere zuwa Najeriya bayan tuhumarta da laifin damfara, kuma yanzu an bayar da umarnin kama ta.

Njoku, dan shekaru 33, ƙwararren ma'aikacin jinya ne da ya je Ingila a matsayin ɗalibi. Ya amsa laifin damfara ta hanyar yin amfani da sunan wani ba bisa ƙa’ida ba.

Lauyansa, Steven Alis, ya bayyana cewa abokinsa ya aikata hakan ne saboda matsin tattalin arziki da kuma kafin a kammala binciken bayanansa na aiki.

Ya ƙara da cewa ma’aikatan asibitin sun kasa gane cewa ba Joyce George ba ce ke aiki, duk da cewa Njoku yana amfani da katin aiki (NHS ID badge) da hoton George a kai.

Mai laifi a magarkama.
Hoton hannun mai laifi a magarkama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotu ta daure Njoku a gidan yarin Ingila

Asirin Njoku ya tonu ne bayan wani mara lafiya ya lura da bambanci a tsakanin hoton da fuskar Njoku, inda ya tambaye shi. Njoku ya ce masa, “Sunana Joyce, amma namiji ne.”

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

Alƙalin kotun, John McGarva, ya yanke masa hukuncin watanni 16 a gidan yari, amma ya dakatar da aiwatar da hukuncin na shekara daya.

Haka kuma, ya umarce shi da ya biya fan 239 (£239) a matsayin kuɗin shari’a da tara, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kotun Amurka ta takaita tsohon jami'in NNPCL

A wani labarin, kun ji cewa wata kotu a Amurka ta bayar da umarni da a kwace kadarar tsohon jami’in NNPC da aka kama da laifin cin hanci da rashawa.

Tun farko dai kotun ta gano cewa tsohon jami'in NNPCL, Paulinus Okoronkwo, ya karɓi $2.1m daga kamfanin mai na Addax Petroleum a matsayin na goro.

Ya karbi kuɗin ne a lokacin da yake aiki a matsayin babban manajan sashen hakar mai a NNPCL domin a ba su lasisin hakar mai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262