Trump Ya Gargaɗi Hamas kan Yarjejeniyar Gaza, Ya Aika Wakili Isra'ila
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar murkushe Hamas idan ta karya yarjejeniyar zaman lafiya da kawarta, Isra'ila
- Mataimakin shugaban kasa, JD Vance ya tafi Isra'ila domin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma da taimakon Qatar
- Wannan na zuwa ne Isra’ila ta zargi Hamas da kin cika alkawarin mayar da gawarwakin mutane 28 da ke hannunta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gargaɗi Hamas cewa za a "rushe ta gaba ɗaya" idan ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakaninsu da Isra’ila.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban kasa JD Vance ke tafiya zuwa Isra’ila domin ƙarfafa wannan yarjejeniya mai rauni.

Source: Getty Images
France24 ta wallafa cewa Shugaban Amurka, Trump, ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a Fadar White House ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump ya gargadi Hamas
RFI ta ruwaito cewa a yarjejeniyar da suka cimma, Hamas ta yi alkawarin ci gaba da zama ta gari domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Gaza.
Ya ce:
"Mun yi yarjejeniya da Hamas cewa za su kasance masu halin kirki, za su zauna lafiya. Idan suka karya wannan, za mu rusa su gaba ɗaya, kuma sun san da hakan."

Source: Twitter
Sai dai duk da tashin hankali da aka samu a karshen mako, bangarorin biyu sun ce har yanzu suna kan bakar yarjejeniyar.
A ranar Litinin, Isra’ila ta tabbatar da cewa Hamas ta mika gawar wani daga cikin mutanen da ke hannunta, wanda hakan ya kai jimillar gawarwaki 13.
Wannan na daga cikin sauran gawarwaki 28 da Hamas ta ɗauki alƙawarin dawo da su ga Isra'ila yayin da ake kokarin kawo karshen hari a zirin Gaza.
Yarjejeniyar Gaza na fuskantar ƙalubale
Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki tun 10 ga Oktoba, ta ƙunshi musayar fursunoni da fatan sake gina Gaza da samar wa jama'arta kwanciyar hankali.
Amma aiwatar da yarjejeniya ya fara fuskantar matsaloli, inda a ranar Lahadi, Isra’ila ta kai hare-hare Gaza, har ta kashe mutane 45.
Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya zargi Hamas da karya yarjejeniyar ta hanyar kai hari, duk da cewa kungiyar ta musanta zargin.
A halin yanzu, mataimakin shugaban kasa JD Vance ya isa Isra’ila domin tattaunawa da Netanyahu kan kalubalen tsaro da damar diflomasiyya da ke gaban su.
Wannan ci gaba ya zo ne a yayin da motoci dauke da kayan agaji ke kokarin shiga Gaza ta hanyar iyakar Rafah, inda ake ci gaba da fuskantar barazanar wargajewar zaman lafiya.
Trump: Ban tsammanin shiga aljanna
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa bai da tabbaci cewa ayyukansa na sulhu, musamman a yankin Gaza, zai iya kai shi aljanna.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
A cikin hira da manema labarai, an tambaye shi ko yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas za ta iya ba shi damar samun rahama bayan mutuwa, Trump ya ce bai sa rai ba.
Wannan furuci na Trump ya zo ne a daidai lokacin da yake gudanar da aiki don tabbatar da cewa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta dore, musamman bayan karuwar kashe bayin Allah.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

