Dubban Falasdinawa Sun Fito Maza da Mata bayan Sojojin Isra'ila Sun Fitar da Sanarwa

Dubban Falasdinawa Sun Fito Maza da Mata bayan Sojojin Isra'ila Sun Fitar da Sanarwa

  • A yau Juma'a, 10 ga watan Oktoba, 2025 shirin zaman lafiya tsakanin kungiyar Falasdinawa watau Hamas da Isra'ila ya fara aiki
  • Rahotanni sun nuna cewa an ga dubban Falasdinawa na fitowa daga wuraren da suka fake, sun tunkari gidajensu a Arewacin Gaza
  • Maza, mata da yara dauke da jakunkuna sun nufi gidajensu a Gaza cikin farin ciki sakamakon zaman lafiyar da aka samu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gaza - Dubban Falasɗinawa ne aka hango suna komawa Arewacin Zirin Gaza da safiyar ranar Juma’a, bayan da sojojin Isra’ila suka sanar da tsagaita wuta.

Rahotanni sun nuna cewa tsagaita wutar ta fara aiki da misalin karfe 9:00 na safe agogon GMT, lamarin da ya sa Falasdinawa da ke gudun hijira suka fara dawowa gidajensu.

Falasdinawa.
Hoton Falasdinawa yayin da suka fara kokarin komawa gidajensu a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Falasdinawa sun fara komawa gida a Gaza

Kara karanta wannan

Trump ya bar mata tsirara, tsarinsa ya jefa masu ciki a barazanar kanjamau

Hotunan da tashoshin labarai na duniya irinsu BBC News suka watsa sun nuna yan Falasdinu, maza, mata da yara, sun fito aun kama hanya dauke da kayan su cikin jakunkuna da keken hannu.

An ga wasu Falasdinawan suna bayyana farin ciki saboda samun damar komawa gida bayan tsawon lokacin da Isra'ila ta shafe tana luguden wuta.

Wannan tsagaita wutar ta zama babbar nasara ga sabon yunkurin diflomasiyya da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kaddamar kwanan nan domin kawo karshen yakin Gaza.

Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniya

Trump ya bayyana ta shafinsa na sada zumunta cewa bangarorin biyu, Isra’ila da Hamas, sun rattaba hannu kan matakin farko na shirin zaman lafiya mai sharudda 20.

Ya ce shirin zaman lafiyar zai dakatar da yaki, sako fursunoni, da kuma janye dakarun Isra’ila, cewar rahoton Reuters.

A karkashin yarjejeniyar, sojojin Isra’ila za su janye daga wasu yankunan Gaza zuwa layin da aka amince da shi a baya, yayin da Hamas za ta sako sauran fursunoni, kimanin 48 gaba ɗaya.

Daga cikin wadanda Hamas za ta saki, ana kyautata zaton mutane 20 suna raye, kuma ana sa ran za ta sako su ne cikin awanni 72 bayan fara tsagaita wutar.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

A madadin haka kuma, Isra’ila za ta saki daruruwan Falasdinawa, ciki har da mutane 250 da aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai da kuma mutum 1,700 da aka kama tun lokacin da rikicin ya fara.

Yan Gaza.
Hoton Falasdinawa na tafiya zuwa Arewacin Gaza bayan tsagaita wuta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, za a bude iyakar da ke tsakanin Masar da Gaza domin ba da damar shiga da kayan agajin jin kai ga Falasdinawa.

Bayana fara aiwatar da shirin zaman lafiya a yau Juma'a, Falasdinawa sun fara tururuwar komawa gidajensu a yankin Arewacin Gaza.

Sheikh Gumi ya aika sako ga Hamas

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi maraba da shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Fitaccen malamin ya bukaci kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta gaggauta sakin duka yahudawan Isra'ila da ke tsare a hannunta ba tare da wani sharadi ba.

Dr. Ahmad Gumi ya ce kuskure ne babba kungiyar Hamas ta tsare mutanen Isra'ila da sunan ta na garkuwa da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262