Hamas da Isra'ila Sun Yi Yarjejeniyar Tsayar da Yaki, za a Daina Kashe Falasdinawa

Hamas da Isra'ila Sun Yi Yarjejeniyar Tsayar da Yaki, za a Daina Kashe Falasdinawa

  • Isra’ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar dakatar da yaki da mayar da fursunoni bayan shekaru biyu ana kai hare-hare a Gaza
  • Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya sanar da wannan mataki a matsayin ɓangare na shirin zaman lafiya da ake kokarin kullawa
  • An yi murna a Isra’ila da Gaza yayin da ake sa ran wannan yarjejeniya za ta kawo ƙarshen zubar da jinin da ake yi a yankin na gabas ta tsakiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Egypt - A ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin Gaza da ya kashe fiye da mutane 67,000, Isra’ila da Hamas sun cimma matsaya ta dakatar da yaki da kuma musayar fursunoni.

Wannan matakin shi ne na farko cikin shirin zaman lafiya da shugaban Amurka Donald Trump ya tsara domin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan

Ecuador: Matasa kusan 500 sun rufe shugaban kasa da jifa da duwatsu

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka da ya sanar da cewa an cimma tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Al-Jazeera ta ce yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawa da aka gudanar a ƙasar Masar, kwanaki bayan cikar shekara biyu da fara kai hare-haren Isra'ila a yankin Gaza ba kakkautawa.

An yi yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an rattaba hannu kan ɓangare na farko na shirin zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Hamas.

A cewarsa, yarjejeniyar za ta tabbatar da sako fursunoni baki daya da kuma janye dakarun Isra’ila daga Gaza.

Trump ya ce wannan mataki zai zama ginshiƙi na zaman lafiya mai ɗorewa, yana mai jaddada cewa nasarar babbar dama ce ga gwamnatin sa da ke fafutukar kawo karshen rikice-rikice.

Isra'ila da Hamas sun rattaba hannu

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta amince da yarjejeniyar a taron ministoci na ranar Alhamis.

A ɓangaren Hamas kuwa, ta tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar da ta haɗa da janyewar sojojin Isra’ila daga Gaza da musayar fursunonin Tel Aviv da na Falasɗinu.

Kara karanta wannan

Saudiyya da kasashen Musulmi 7 na maraba da amincewar Hamas kan zaman lafiya da Isra'ila

Kungiyar ta ce jinin al’ummar Gaza ba zai tafi a banza ba, domin za su ci gaba da fafutukar neman ‘yancin kai da cikakken ikon mulkin kai.

Ana murnar daina yaki a Gaza, Isra'ila

Rahoton Reuters ya nuna cewa bayan sanarwar yarjejeniyar, al’umma a Gaza da Isra’ila sun yi murna da hakan.

Mutane da dama sun bayyana farin cikinsu da fatan cewa wannan lokaci ne na sabuwar rayuwa bayan shekaru na zubar da jini da tashin hankali.

Shugaban Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Hoton wani coci da Isra'ila da kaiwa hari a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani mazaunin Khan Younis, Abdul Majeed Abd Rabbo, ya ce:

“Alhamdulillah, mun gaji da zubar da jini da kisa. Ba ni kaɗai na ji daɗi ba, dukkan Gaza da duniya suna murna da wannan sulhu.”

Rahotanni daga hukumomin Gaza sun nuna cewa fiye da mutane 67,000 ne suka mutu a hare haren da Isra'ila ta kai musu.

Kasashe sun yi murna da sulhu a Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa kasashe da dama sun nuna farin ciki da yadda aka fara tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila.

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Saudiyya da wasu kasashen Musulmi a duniya sun yi fatan alheri kan tattaunawar da ake a Masar.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sa Isra'ila ta fara shirin tsagaita wuta kan Gaza

Shugaban Amurka ya bayyana cewa yana fatan tattaunawar za ta kawo karshen zubar da jinin da aka shafe shekaru ana yi a Gaza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng