Najeriya na cikin Hadari da WHO Ta Tabbatar da Bullar Cutar Chikungunya a Kasashe 40

Najeriya na cikin Hadari da WHO Ta Tabbatar da Bullar Cutar Chikungunya a Kasashe 40

  • Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargadi kasashen duniya ciki har da Najeriya da su dauki matakan kariya dada cutar Chikungunya
  • WHO ta tabbatar da cewa zuwa watan Satumba, 2025, zazzabin wanda sauro ke yadawa ya shiga kasashe 40
  • Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bukaci yan Najeriya su kula da tsaftace muhalli da kuma maganin sauro a gidajensu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - A ranar Talata, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna damuwa kan sake bullar cutar cutar chikungunya, wani zazzabi mai zafi da sauro ke yadawa, a wasu kasashe.

WHO ta ce duk da wasu kasashe sun samu karuwar mutanen da ke kamuwa da wannan cuta, wasu kasashen kuma cutar ta fara ja baya.

Sauro.
Hoton sauron Aedes da ke yada cutar zazzabi ta Chikungunya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukumar ta ce a sherarar 2025, sama da mutum 445,000 ake zargin suna ɗauke da cutar ko kuma aka tabbatar suna da ita, wanda daga cikinsu mutane 155 sun mutu, in ji Premium Times

Kara karanta wannan

Maryam Sanda ta shiga jerin wadanda aka yafewa, Tinubu ya fadi dalilin yafe mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rahoton da ta fitar a ranar Talata, WHO ta ce an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar a wasu yankuna, yayin da wasu yankunan kuma aka samu raguwa.

WHO ta gargadi kasashen duniya

Sai dai ta gargadi cewa har yanzu akwai yiwuwar yaduwar cutar zuwa wuraren da babu ita, domin matafiyan da suka kamu da ita na iya shigar da ita kasashen da ke da sauron da ake kira Aedes.

Zuwa watan Satumban 2025, an tabbatar da cutar ta shiga ƙasashe 40. Yankin Amurka ne ya fi samun mafi yawan masu kamuwa da cutar, sannan Turai.

Tsakanin watan Janairu zuwa Satumba, WHO ta samu rahoton mutum 263,592 da ake zargin cutar ta kama da 181,679 da aka tabbatar suna ɗauke da ita, 155 daga ciki sun mutu.

Kasashen da cutar ta shiga a Afirka

Yayin da wasu yankuna kamar Afirka suka samu raguwa idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, yankin Amurka, Turai da kuma wasu sassan Kudancin Asiya sun fuskanci ƙaruwar kamuwa da cutar.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta gindaya sharudda masu tsauri ga musulman da za su tafi aikin Hajjin 2026

A Afirka, an tabbatar da bullar cutar a Kamaru, Kenya, Mauritius da Senegal, inda Mauritius ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar.

A Kenya, hukumomi sun tabbatar da barkewar cutar a lardin Mombasa a watan Yuni, amma babu karin rahoton sababbin masu kamuwa bayan watan Yuli.

Alamomin zazzabin cutar Chikungunya

A rahoton Reuters, sauron Aedes aegypti da Aedes albopictus ne suke yada wannan cuta, kuma wannan kalar sauron ne ke yada zazzabin dengue da kwayar Zika.

Alamomin cutar na bayyana kwanaki hudu zuwa takwas bayan cizon sauron da ke ɗauke da ita, inda mutum zai ji zazzabi, ciwon tsoka, kaikayin fata, da tsananin ciwon gaɓoɓi da kan iya ɗaukar makonni har ma watanni.

Mafi yawancin wadanda suka kamu suna murmurewa gaba ɗaya, sai dai cutar kan tsananta ga jarirai, tsofaffi da kuma masu wasu matsalolin lafiya tun da.

Hadarin da Najeriya ke fuskanta

A watan Agusta, Hukumar Yaki da Cututtuka ta Kasa, NCDC ta tabbatar cewa ba a samu rahoton bullar cutar chikungunya a Najeriya ba tukuna.

Amma ta gargadi cewa yanayin muhalli na yanzu, musamman ambaliyar ruwa da ke faruwa a wasu jihohi, na iya kawo bullar cutar.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun shiga Kaduna, sun gano mabuyar masu garkuwa da mutane

Hukumar ta bukaci jihohi su ƙarfafa sa ido, kawar da sauro, da inganta dakin gwaje-gwaje a matsayin shirin tunkarar lamarin.

Shugaban hukumar NCDC, Dr. Olajide Idris.
Hoton Shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dr. Olajide Idris. Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

Ta tunatar da jama’a cewa matakan kariya daga kwalara, dengue da zazzabin cizon sauro, irin su kawar da kwata, amfani da ragar sauro, maganin sauro da tsaftace muhalli, suna da tasiri wajen kariya daga cutar chikungunya.

WHO ta bukaci ƙasashe da su ƙarfafa sa ido kan cututtuka, kawar da sauro da kuma inganta hanyoyin gano cuta domin gano bullar cuta da wuri tare da tunkarar ta yadda ya dace.

Wani malamin lafiya da ke aiki a asibitin gwamnati a Katsima, Muhammad Bello ya shaida wa Legit Hausa cewa ana samun karuwar masu fama da zazzabi a asubitoci.

Ya ce kamar yadda NCDC ya fada, wannan zazzabin na iya shigowa Najeriya matukar mutane ba su dauki matakin kariya ba.

Muhammad ya ce:

"Muna da kalar sauron da ke yada wannan cuta, kuma idan ka duba mutane na mu'amala ba tare da bin matakan kariyar lafiya ba, wannan hadari ne babba.

Kara karanta wannan

Trump ya bar mata tsirara, tsarinsa ya jefa masu ciki a barazanar kanjamau

"Ya kamata mutane su rika taka tsantsan, duk wanda aka ga ya nuna alamun kamuwa da cutar, a gaggauta kai shi babban asibiti da za a killace shi har sai an yi gwaje-gwaje."

Mutum 2 sun kamu da Ebola a Abuja?

A wani labarin, kun ji cewa hukumar NCDC ta tabbatar da ba a samu cutar Ebola ko Marburg a jikin mutane biyu da ake zargin sun kamu da cututtukan ba a Abuja.

Hukumar ta ce an gudanar da gwaje-gwaje na farko kan mutanen da ake zargin, kuma sakamakon bai nuna su na dauke da Ebola ba.

Ebola cuta ce mai tsanani wacce take haddasa zubar jini a jiki, kuma kashi 25 zuwa 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita na mutuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262