Trump Ya Umarci Netanyahu Ya Gaggauta Daina Luguden Wuta a Gaza
- Shugaba Donald Trump ya bukaci Isra’ila ta dakatar da luguden wuta a Gaza domin bai wa Hamas damar sakin fursunoni cikin aminci
- Hamas ta ce ta amince da wasu muhimman bangarori na shirin zaman lafiya guda 20 da Trump ya gabatar tare don kawo karshen hare hare
- Kungiyar ta kuma nuna shirinta na mika mulkin yau da kullum na hukumomin Gaza ga wata kungiyar ’yan Falasdinu masu zaman kansu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Donald Trump, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta gaggauta dakatar da luguden wuta a Gaza domin bai wa Hamas damar sakin fursunoni cikin aminci da sauri.
Wannan sanarwa ta zo ne jim kadan bayan da Hamas ta ce ta amince da wasu bangarorin shirin zaman lafiya da Trump ya gabatar a makon da ya gabata.

Source: UGC
Rahoton The Independent na ranar Juma’a, 3, Oktoba, 2025 ya ce Trump ya bayyana cewa Hamas ta nuna shirinta na shiga yarjejeniyar musayar fursunoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hamas ta amince da sako fursunoni
Hamas ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa za ta saki dukkan fursunonin Isra’ila, a raye ko a mace, bisa tsarin musayar da aka gindaya a shirin da Trump ya gabatar.
Kungiyar ta ce ta gode wa kokarin kasashen Larabawa wajen neman kawo karshen yakin da ake yi a Gaza da kuma shigar da agaji cikin gaggawa.
Sanarwar ta kuma nuna cewa Hamas ta yarda ta mika ragamar gudanar da harkokin yau da kullum na Gaza ga wata kungiyar ’yan Falasdinu masu zaman kansu.
Shirin Trump na zaman lafiya a Gaza
Shirin zaman lafiyan da shugaban Amurka, Trump ya gabatar ya kunshi matakan kawo karshen rikicin Gaza.
Daga ciki akwai batun musayar fursunoni, tsagaita wuta, da samar da tsarin mulki na wucin gadi a Gaza karkashin wakilan Falasdinu.

Kara karanta wannan
Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa
Sai dai akwai muhimmin bangare na shirin da bai samu amincewar Hamas ba, inda aka bukaci kungiyar ta daina daukar makamai gaba daya.

Source: AFP
Matsayar Hamas kan daukar makamai
Babban jami’in Hamas, Mousa Abu Marzouk ya bayyana a wata hira da Al Jazeera cewa kungiyar ba za ta amince ta ajiye makamai ba sai bayan Isra’ila ta kawo karshen mamayarta a Gaza.
Duk da haka ya ce Hamas na shirye ta mika makaman nata ga wata gwamnatin Falasdinu da za ta karbi ragamar mulkin yankin a nan gaba.
Ya kara da cewa kungiyar ta nuna shirin shiga tattaunawa kai tsaye ta hannun masu shiga tsakani domin fayyace sauran bayanai da suka rage.
Wannan na nufin har yanzu akwai muhimman bangarori da ke bukatar karin tattaunawa kafin cimma matsaya ta karshe.
An saki shugaban Falasdinawan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta ta saki shugaban Falasdinawa da aka kama a Agustan 2025, Ramzy Abu Ibrahim.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'an 'yan sanda ne suka kama Abu Ibrahim a gidan shi da ke birnin tarayya, Abuja.
Tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yaba da sakin shugaban yayin da suka gana bayan fitowar shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

