Zarge Zargen Karuwanci: Kotu Ta Yanke wa Fitaccen Mawaki Hukuncin Daurin Wata 50

Zarge Zargen Karuwanci: Kotu Ta Yanke wa Fitaccen Mawaki Hukuncin Daurin Wata 50

  • An yanke wa mawaki, Sean “Diddy” Combs hukuncin daurin fiye da shekaru huɗu a gidan yari kan laifuffukan da suka shafi karuwanci
  • Alƙali ya ce Combs ya yi amfani da iko da ƙarfi wajen cutar da tsofaffin 'yan matasan, ciki har da wacce ta ba da shaida a kotu
  • Lauyoyi sun nemi a saki mawakin saboda ya dade a tsare, amma kotu ta ƙi, tana mai cewa laifuffukansa sun jefa mata a mawuyacin hali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Kotu ta yanke wa shahararren mawakin hip-hop, Sean “Diddy” Combs, hukuncin zaman gidan yari na fiye da shekaru huɗu kan tuhumar da ta shafi karuwanci a Amurka.

Alƙali Arun Subramanian ya yanke masa hukuncin ne duk da roƙon da mawaki Sean Combs ya yi a kotu, inda ya nemi a sassauta masa hukuncin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun tilasta rufe makarantu 180 a Arewa

Kotu ta kama fitaccen mawakin amurka, Sean Diddy Combs da laifuffukan da suka shafi karuwanci
Hoton fitaccen mawakin hip-hop, Sean 'Diddy' Combs da kotu ta kama da laifuffukan karuwanci a Amurka. Hoto: @DiddyTrialWatch
Source: UGC

Abin da kotu ta tabbatar kan mawaki Diddy

A watan Yuli ne aka samu mawaki Sean Combs, da laifin kai mutane zuwa wurare daban-daban a Amurka da ƙasashen waje domin yin karuwanci, inji rahoton Sky News.

Wadanda yake kai wa sun hada da tsofaffin 'yan matansa da suka yi soyayya da maza masu neman maza da mata, wanda hakan ya saɓa wa dokokin Amurka.

Sai dai kotu ta wanke shi daga manyan tuhumomi da suka hada da safarar mata don karuwanci, waɗanda da an tabbatar da su, zai iya fuskantar daurin rai-da-rai.

Shaidun da aka gabatar yayin shari’a

Shaidu sun haɗa da Cassie Ventura, tsohuwar budurwarsa, wacce ta bayyana yadda aka tilasta mata shiga cikin al’amuran “cire kaya da jima'i” tare da wasu maza.

An kuma nuna wa alƙalai bidiyon mawaki Sean Combs yana jan Cassie Ventura a kasa, yana bugunta a ɗakin otal a Los Angeles a 2016.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda wani shugaban APC ya mutu yana cikin raba N50,000

Cassie ta rubuta wasiƙa ga alƙali kafin yanke hukuncin, inda ta bayyana mawakin a matsayin “mayaudari” tare da cewa har yanzu tana firgita idan ta tuna shi.

Hukuncin da alkalin kotu ya yanke

Mawaki Sean Combs, wanda ya kafa Bad Boy Records kuma ya lashe lambar yabo ta Grammy, yana fuskantar daurin shekaru 20 a kurkuku kan laifuffukan da aka tabbatar.

Kotu ba ta karfi korafin lauyoyin Sean Diddy na sakinsa, inda alkali ya yanke masa zaman gidan yari na watanni 50
Hoton fitaccen mawakin hip-hop, Sean 'Diddy' Combs da kotu ta kama da laifuffukan karuwanci a Amurka. Hoto: @DiddyTrialWatch
Source: Instagram

Masu shigar da ƙara sun nemi a yanke masa akalla shekaru 11 a kurkuku, yayin da lauyoyinsa suka nemi ya sami ’yanci nan da nan saboda lokacin da ya riga ya shafe a tsare tun bayan kama shi fiye da shekara guda.

Alƙalin dai ya ƙi karbar korafin lauyoyin mawakin, yana mai cewa Sean Combs ya yi amfani da iko da ƙarfi wajen cutar da matan da yake ikirarin yana ƙaunarsu.

Mai shari'a Arun Subramanian ya yanke wa Sean Combs hukuncin watanni 50 a gidan yari, ma'ana shekaru hudu da watanni biyu, in ji rahoton BBC.

Alkalin kotun ya ce hukuncin ya yi dai dai idan aka yi la'akari da girman laifuffukan mawakin, sannan an yanke masa hukuncin ne kan laifuffuka biyu da suka shafi kai mata da maza ana karuwanci da su

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Atiku ya caccaki Tinubu kan yunwa da tsaro, ya bukaci kifar da APC

Kotu ta daure mawaki Hamisu Breaker

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ya yanke wa Hamisu Breaker hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari bisa laifin cin zarafin Naira a Jigawa.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Breaker tare da G-Fresh Al'Ameen bayan an gan su suna lika Naira yayin bukukuwa, kuma sun amsa laifuffukansu.

Kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari ko kuma biyan tarar N200,000 ga mawaki Hamisu Breaker da G-Fresh, yayin da EFCC ke ci gaba da yaki da lika kuɗi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com