Flotilla: Isra'ila Ta Kai Hari kan Masu kai Agaji Gaza, Wasu Jiragen Ruwa Sun Kubuta
- Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta kashe mutane 73 a Gaza tare da cafke masu fafutukar Flotilla da ke shirin kai agaji
- Sanata Chris Andrews na kasar Ireland na daga cikin waɗanda aka tsare, Sinn Fein ta ce an kama shi ba bisa ƙa’ida ba
- Hare-haren sun jawo zanga-zanga a kasashen Turai, yayin da wasu ƙasashe suka kira matakin na Isra’ila babban laifi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza - Aƙalla mutane 73 ne suka mutu a Gaza bayan hare-haren dakarun Isra’ila, lamarin da ya kara tsananta tashin hankali a yankin.
Wannan na zuwa ne yayin da jiragen ruwa na agaji suka shiga hannun sojojin Isra’ila a cikin ruwan kasa da kasa a hanyar kai agaji Gaza.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya ce an kama ɗaruruwan masu fafutuka da ke kan jiragen ruwan, ciki har da fitacciyar mai fafutuka, Greta Thunberg, da kuma Sanatan Ireland, Chris Andrews.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya jawo martani daga ƙasashen duniya, ciki har da kira daga shugabannin Turai da Amurka da suka ce Isra’ila ta karya dokokin kasa da kasa.
Isra'ila ta tsare 'yan gwagwarmayar Flotilla
Jam’iyyar Sinn Fein ta kasar Irelan ta tabbatar da cewa Sanata Chris Andrews ya shiga hannun sojojin Isra'ila a hanyar kai tallafi Gaza.
Rahoton Reuters ya nuna cewa jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin Ireland da ta tashi tsaye wajen ganin an sako shi da sauran ’yan ƙasarsu guda 22 da ke cikin jirgin.
Shugaban Ireland, Michael D Higgins, ya ce matakin ya sabawa doka, musamman ma ganin cewa jiragen sun ɗauko abinci, magunguna da ruwan sha ne domin taimakawa fararen hula.
Jiragen ruwan da Isra'ila ta kama
A wani bidiyo da ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta wallafa, an ga Greta Thunberg tana zaune a saman jirgin da dakarun Isra’ila suka kewaye.
Rahotanni sun ce jiragen ruwa guda 13 ne aka cafke, yayin da wasu 30 ke ci gaba da kokarin isa Gaza.

Source: Getty Images
An bayyana cewa jiragen ruwan suna cikin shirin Global Sumud Flotilla, wanda ya haɗa mutane sama da 500 daga ƙasashe daban-daban da nufin kai kayan agaji ga al’ummar Gaza.
Martanin ƙasashen duniya ga Isra'ila
Matakin Isra’ila ya tayar da zanga-zanga a kasashen Greece, Italy da Belgium, inda dubban jama’a suka fito kan tituna suna nuna goyon baya ga Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana harin a matsayin “ta’addanci”, yayin da shugaban ƙasar Colombia, Gustavo Petro, ya kori dukan jakadun Isra’ila daga ƙasarsa.
Petro ya kuma soke yarjejeniyar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu, yana mai kiran kamun mutanensa biyu a cikin jirgin a matsayin sabon laifin kasa da kasa.
Isra'ila ta kashe Kiristoci a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa wani rahoto ya nuna cewa kasar Isra'ila ta kashe Kiristoci da dama a hare haren da ta kai Gaza.
Rahoton ya bayyana cewa Isra'ila ta ruguza coci coci, gidaje da wasu wurare da Kiristocin da ke zaune a Gaza ke amfani da su.
An yi martanin ne bayan Benjamin Netanyahu ya yi magana a zauren majalisar dinkin duniya cewa yana kare Kiristoci a Gabas ta Tsakiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


