Damfarar Soyayya: An Kama Dan Najeriya da Ya Yaudari 'Yan Mata Sama da 100 a Indiya

Damfarar Soyayya: An Kama Dan Najeriya da Ya Yaudari 'Yan Mata Sama da 100 a Indiya

  • Rundunar 'Yan Sanda a Birnin Delhi ta kama wani dan Najeriya bisa zargin yaudarar mata sama da 100 a kasar India
  • Binciken yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya damfari matan makudan kudi bayan sun kulla soyayya
  • 'Dan Najeriyan ya shiga India ne tun 2019 amma bayan bizarsa ta kare sai ya shiga harkallar damfarar soyayya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

New Delhi, India - ‘Yan sandan birnin Delhi sun kama wani ɗan Najeriya mai shekara 29 da ake zargin ya yaudari mata fiye da 100, ya karbi kudade daga hannunsu a Indiya.

Yan sandan sun ce ya yi amfani da sunan wani ɗan kasuwa ɗan asalin Koriya mazaunin Birtaniya a wata manhajar ta soyayya da kulla aure.

Yan sandan India.
Hoton yan sandan India a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar jaridar Hindustan Times, wanda ake zargin sunansa Stephane amma yana amfani da sunaye na ƙarya “Dominic” da “Duck Young,” an kama shi a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Dakarun sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan ta'adda a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan India sun cafke dan Najeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun cafke matashin dan Najeriyan a wani ɗakin haya da yake zaune a Tilak Nagar, da ke yammacin birnin Delhi.

Mahukunta sun ce wanda ake zargin ya yi amfani da tsarin damfarar soyayya, inda su ke amfani da shafukan sada zumunta da na soyayya don ruɗar da mata.

Yan sanda sun gano cewa, abokan aikin da dan Najeriya ya hada baki da su, sun rika kiran matan da sunan cewa su jami'an gwamnati ne.

Yadda dan Najeriya ya damfari mata a India

Rahoton bincike ya nuna cewa sun rika neman kudi daga hannun matan da sunan za su wanke Stephane daga wani zargi na karya.

'Yan matan sun rika tura kudin da aka nema da tunanin su na taimakon saurayinsu ko ma wanda za su aura bayan kulla soyayya a kafar sada zumunta.

Asirin 'yan damfarar ya fito fili ne bayan wata mace mai suna Anjali ta kai rahoton damfarar da aka mata na rufi 48,500.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga har gida sun datsa Sarkin Fulani da adda a Neja

Ta bayyana cewa “Duck Young” ya yi ikirarin cewa an tsare shi a filin jirgin saman Mumbai, daga baya ta samu kiran wasu mutanen da suka yi ikirarin jami’an hukumar shige da fice ne, suka nemi ƙarin lakh biyu.

Abubuwan da aka kwato daga hannunsa

‘Yan sandan sun gano cewa Stephane ta hanyar bin diddikin kira, asusun banki da kuma ayyukansa a kafafen sada zumunta.

Lokacin da aka kama shi, an samu waya cike da bayanan ƙarya da hirarraki da mata fiye da 100.

Subun dan Najeriya ta cika a India.
Hoton wani wanda aka kama bisa zargin aikata laifi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A yayin bincike, ya amsa cewa ya shiga Indiya tun 2019 da bizar yawon buɗe ido na watanni shida kuma ya yi amfanni da fasfon Côte d’Ivoire domin guje wa takunkumin da aka sanya kan ‘yan Najeriya a wancan lokaci.

Bayan bizar ta ƙare kuma kuɗinsa suka ƙare, sai ya farar harkar yaudarar 'yan mata ta yanar gizo, in ji rahoton Leadership.

'Dan Najeriya ya damfari Amurkawa

A wani labarin, kun ji cewa an kama dan Najeriya mai suna, Ehis Lawrence Akhimie da laifin damfarar mutane Dala miliyan 6 a kasar Amurka

Bayan ta tabbatar da yaaikata laifin da ake tuhumarsa, kotun Amurka ta yanke wa dan Najeriya hukuncin daurin watanni 97 a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Kanawa sun fusata, ana zargin 'yan sanda da ajalin wani limami

Ofishin Antoni Janar ya bayyana yadda Akhimie tare da abokansa suka yaudari Amurkawa da sunan za a fito masu da kudin gadon yan uwansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262