Sarki Sanusi II Ya Fadi abu 1 da Najeriya Ke Bukata don Farfado da Tattalin Arziki

Sarki Sanusi II Ya Fadi abu 1 da Najeriya Ke Bukata don Farfado da Tattalin Arziki

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnati da masu zaman kansu su haɗa kai don bunkasa tattalin arzikin Najeriya
  • Sanusi II ya ce Najeriya ba za ta iya dogaro kacokan da kuɗin gwamnati ba, inda ya ce masu zuba jari su ne ginshiƙin farfado da tattali
  • Mai martaba sarkin Kanon ya bayyana haka ne a wani babban taro a birnin New York, a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 80

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nemi a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangaren masu zaman kansu.

Sanusi II ya bayyana cewa, yaukaka dangantaka tsakanin gwamnati da masu zaman kansu zai sauya tattalin arzikin Najeriya cikin gaggawa.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nemi gwamnati ta hada kai da masu zaman kansu don habaka tattalin arziki.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II tare da attajirin duniya, Bill Gate a wani bangare na taron UNGA a Amurka. Hoto: @KanEmirateMedia
Source: Twitter

'Hanyar farfado da tattali' - Sanusi II

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

Mai martaba sarkin ya bayyana haka ne a wani babban taro da aka gudanar a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York, Amurka, inji rahoton Punch.

Sarki Sanusi II ya ce jarin masu zaman kansu shi ne ginshiƙin da zai iya buɗe damar tattalin arzikin Najeriya da kuma dorewar sauye-sauyen da ake aiwatarwa yanzu.

A cewarsa sarkin na Kano:

“Najeriya ba za ta iya dogaro kacokan da kuɗin gwamnati ba. Tilas a bai wa ɓangaren masu zaman kansu muhimmanci wajen haɓaka tattalin arziki da jawo hannun jarin da ake buƙata.”

Sanusi II: Fa'idar haɗin gwiwar gwamnati da PPP

Taken taron da Sanusi II ya halarta shi ne, “Jawo masu zuba jari don ci gaban tattalin arziki da musayar al’adu.”

An rahoto cewa an gudanar da taron ne a dakin taro na kwalejin fasahar zamantakewa ta Henry George da ke Manhattan, Amurka.

A cewar sanarwar da shugaban jam'iyyar APC na Amurka, Farfesa Tai Balofin, ya fitar ranar Laraba, hukumar NBTI ta Najeriya, Newday International, kungiyar kwararru 'yan Najeriya mazauna waje da APC USA/CDC ne suka shirya taron.

Kara karanta wannan

'Kowa ya shirya,' Amabliyar ruwa za ta shafi yankuna 69 a Kano, Borno da jihohi 13

A wajen taro, Sarki Sanusi II ya bayyana haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) a matsayin ginshiƙi na ci gaban Najeriya, yana mai jaddada cewa ba za a iya samun ci gaba mai ma'ana ba tare da shi ba.

A cewar sarkin, gina ababen more rayuwa na zamani, masu inganci, da tsawon rai yana da matukar muhimmanci don biyan burikan miliyoyin 'yan Najeriya.

Masu ruwa da tsaki sun tofa albarkacin baki

Da yake goyon bayan kiran Sanusi II kan haɗin gwiwa, shugaban hukumar NBTI, Dr. Kazeem Kolawole Raji, wanda Tunde Doherty ya wakilta, ya ce dabarun shigar da fasaha a cikin masana'antu yana ƙarfafa ci gaban ƙere-ƙere.

“Ta hanyar shigar da fasaha, ba wai kawai muna haɓaka ƙere-ƙere ba ne, muna samar da hanyoyin ci gaba mai dorewa a fannin noma, makamashi, da sauran muhimman sassa."

- Dr. Kazeem Kolawole Raji.

Haka nan shugaban Newday International kuma shugaban APC USA, Farfesa Tai Balofin, ya bayyana harkar gidaje da gine-gine a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki.

Farfesa Tai Balofin ya ce akwai dama mai yawa da Najeriya da Amurka za su iya amfani da ita wajen jawo jarin waje a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya hadu da ministocin Tinubu a majalisar dinkin duniya

Sarkin Kano, Sanusi II ya ce arzikin Najeriya zai habaka idan aka samu masu zuba jari.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayin da yake fitowa daga fada. Hoto: @KanEmirateMedia
Source: Twitter

Matan Najeriya sun nemi a basu karin dama

The Guardian ta rahoto, uwargidan gwamnan jihar Osun, Hajiya Titilola Adeleke, ta jaddada muhimmancin hada mata da yara a cikin tsare-tsaren tattalin arziki.

Hajiya Titilola Adeleke ta ce:

“Ta hanyar shirye-shiryen ilimi, kiwon lafiya da noma, muna karfafa mata da yara. Zuba jari mai inganci zai kara bunkasa wadannan shirye-shirye kuma ya ruguza wariyar jinsi domin samun ci gaba mai dorewa.”

Taron ya kuma samu halartar matan gwamnoni irin su Farfesa Olufolake Abdulrazaq ta Kwara, Fatima Mohammed Bago ta Neja, Zulaihat Dikko Radda ta Katsina, da Huriyya Dauda Lawal ta Zamfara.

UNGA: Sanusi II ya hadu da ministocin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya gabatar da jawabi a taron Goalkeepers 2025 a birnin New York kan kare rayuwar yara.

Sarkin ya gana da attajirin duniya, Bill Gates da kuma Fasto Rick Warren inda suka tattauna dabarun kawo ci gaba mai dorewa a Kano da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

Sanusi II ya halarci taron Afrika a majalisar dinkin duniya, tare da ganawa da Sarauniya Máxima game da hada-hadar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com