Trump Ya Yi wa Shugabannin Iran da Suka Shiga Amurka Rashin Mutunci
- Amurka ta sanya wa jami’an Iran da suka halarci taron majalisar dinkin duniya takunkumi na musamman kan sayen kaya
- Rahotanni sun bayyana cewa takunkumin Amurkan ya shafi kayan alatu kamar agogo da wasu abubuwan da aka ayyana
- Hukumar diflomasiyya ta Amurka ta ce matakin na nuna goyon baya ga talakawan Iran da ke fama da fatara da karancin albarkatu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Gwamnatin Amurka ta hana jami’an Iran da ke halartar taron koli na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York damar yin sayayya a shaguna da dama.
Rahotanni sun nuna cewa an hana su sayayya ne a manyan shaguna da kuma wuraren sayar da kayan alatu.

Source: Getty Images
Rahoton the Guardian ya nuna cewa matakin na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na tsarin matsin lamba da gwamnatin Amurka ta ɗauka kan Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Thomas Pigott, ya bayyana cewa ba za a bar shugabannin Iran su saye kayan da sauran 'yan kasar ba za su iya saye ba.
Kayan da Amurka ta hana Iran saye
Sanarwar da aka wallafa ta bayyana cewa jami’an Iran ba za su iya sayen kayayyaki ba tare da izinin gwamnatin Amurka ba, musamman idan darajarsu ta kai sama da $1,000.
Kayan da abin ya shafa sun haɗa da agogo, na’urorin lantarki, alƙaluman rubutu masu tsada, da kuma motoci masu darajar fiye da $60,000.
Har ila yau, an hana jami’an ziyartar manyan shaguna kamar Costco, Sam’s Club da BJ’s Wholesale Club, inda ake samun kayayyaki da yawa a kan farashi mai sauƙi.

Source: Getty Images
Waɗannan shagunan na daga cikin wuraren da jami’an Iran ke sayen kaya domin turawa gida saboda takunkumin tattalin arziƙi a ƙasarsu.
Takunkumin kasar Amurka kan Iran
Dama dai Amurka ta hana shigar da kayayyaki daban-daban Iran tare da dakile damar Teheran wajen sayar da man fetur da sauran kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Tun daga lokacin da Shugaba Donald Trump ya hau mulki a bana, ya ƙara matsin lamba kan Iran, har ma ya ba da umarnin kai hare-haren bama-bamai da makamai masu linzami kan kasar.
Saƙon Amurka ga al’ummar Iran
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce manufar su ita ce hana jami’an Iran amfani da damar diflomasiyya wajen sayen kayayyaki da jama’ar ƙasar ba za su iya samu ba.
Rahoton NBC News ya nuna cewa sanarwar ta ce:
“Da wannan mataki, muna aika saƙo kai tsaye: Lokacin da Amurka ta ce tana tare da jama’ar Iran, muna nufin hakan da gaske,”
Matakin na nuni da cewa Iran ce kaɗai ƙasar da aka ware a ƙarƙashin wannan tsari na hana jami’ai cin gajiyar tafiyar diflomasiyya wajen yin sayayya a Amurka.
Sanusi II ya je taro kasar Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya halarci taron majalisar dinkin duniya a Amurka.
Sarkin ya gana da wasu ministocin Najeriya da suka hada da Yusuf Maitama Tuggar da Muhammad Badaru Abuabakar.
Baya ga 'yan Najeriya, Sanusi II ya tattauna da Bill Gates kan wasu lamura da suka shafi jihar Kano da Najeriya baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

