Watanni bayan Yakin Kwanaki 12, Kasar Iran Ta Hukunta 'Munafikin' da Ya Yiwa Isra'ila Aiki
- An yanke wa wani mutumi, Babak Shahbazi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Iran bayan kama shi da laifin yiwa Isra'ila leken asiri
- Hukumomin Iran sun zartar da wannan hukunci kan Shahbazi, kuma sun lashi takobin hukunta duk wanda ya hada kai da Isra'ila
- Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan musayar wutar da ta faru tsakanin kasashen biyu, wanda ta shafe kwanaki 12
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kasar Iran - Hukumomin Iran, a ranar Laraba, sun aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum da aka same shi da laifin yiwa Isra'ila leƙen asiri.
Iran ta bayyana cewa ta kama mutumin da laifin tura wa hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad, bayanan sirri, wanda hakan babban laifi ne a dokar jamhuriyar musulunci.

Source: Twitter
Iran ta hukunta dan leken asirin Isra'ila

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya ya jefa kansa a badakalar 'kudin gado' a Amurka, kotu ta yanke hukunci
Jaridar Reuters ta ruwaito cewa an rataye mutumin mai suna, Babak Shahbazi, da safe bayan kammala dukkan matakan shari’a tare da tabbatar da hukuncinsa daga Kotun Koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar dillancin labarai ta Iran, IRNA, ta bayyana cewa an samu Shahbazi da laifin leƙen asiri da kuma haɗin gwiwa da Isra’ila, inda ake zargin ya yi hulɗar musayar bayanai da wasu jami’an Mossad.
An kuma tuhume shi da ƙoƙarin sayar da bayanan sirri na manyan jami’an Iran ga wani jami’in Mossad mai suna Esmaeil Fikri, wanda shi ma aka kashe a watan Yuni 2025 bisa leƙen asiri ga Isra’ila.
Yadda Iran ta kama mai yiwa Isra'ila aiki
A cewar jaridar Times of Israel, hukumomin Iran sun bayyana cewa Shahbazi ya gana da jami’an Isra’ila ta intanet, kuma ya samu horo daga Mossad, sannan ya yi ƙoƙarin tattara bayanai kan manyan jami’ai da kuma muhimman wuraren a Iran.
Kotun Iran ta yanke masa hukuncin kisa bisa manyan laifuka na “fasadi a doron ƙasa” da kuma “yaƙi da Allah.”
Rahotannin sun ce Shahbazi yana aiki a fannin ƙira da injinan sanyaya wuri a kamfanonin da ke da alaƙa da harkokin sadarwa, soja da tsaro.

Kara karanta wannan
Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi
Wannan aiki ya ba shi damar shiga wuraren da ke da bayanai masu muhimmanci, abin da ake zargin ya yi amfani da shi wajen bai wa Mossad bayanai.

Source: Twitter
Iran ta sha alwashin hukunta yan leken asiri
Hukuncin kisan na zuwa ne yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Isra’ila da Iran bayan yaƙin kwanaki 12 da suka yi a watan Yuni.
Tun wannan lokaci dai Iran ta sha alwashin ɗaukar tsauraran matakai kan duk wanda aka kama da laifin haɗin gwiwa da Isra’ila.
An zargi Isra'ila da aikata babban laifi a Gaza
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dinkin Duniya ta gano yadda Isra’ila ta aikata kisan kare dangi a Gaza bisa shaidu da aka tattara.
Kwamitin bincike da Majalisar ta kafa ya kammala tattara bayanai da shaidu, ya kuma tabbatar da cewa Isra'ila ta aikata laifi a zirin Gaza.
Rahoton ya bayyana cewa shaidun da suka tattara sun nuna an yi niyya a halaka al’ummar Palasɗinu a Gaza ta hanyar kisa da kuma tsananta musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng