A Karshe, Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Isra’ila Ta Yi Kisan Kare Dangi a Gaza
- Kwamitin bincike na majalisar dinkin duniya ya ce Isra’ila ta aikata kisan kare dangi a Gaza bisa shaidu da aka tattara
- Rahoton ya bayyana cewa Isra’ila ta aikata fiye da guda hudu daga cikin manyan laifuffukan da yarjejeniyar 1948 ta tanada
- Hakan na zuwa ne bayan sojojin kasar Isra'ila na cigaba da kashe mutane a Gaza da kai hari wasu kasashe kamar Qatar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza - Sabon rahoto da kamitin bincike na majalisar dinkin duniya ya fitar ya zargi Isra’ila da aikata kisan kare dangi a Gaza.
Rahoton ya bayyana cewa shaidun da suka tattara sun nuna an yi niyya a halaka al’ummar Palasɗinu a Gaza ta hanyar kisa da kuma tsananta musu.

Source: Getty Images
Shugabar kwamitin, Navi Pillay, ta bayyana cewa duk shaidun da aka tattara sun nuna akwai manufar shafe al’ummar Gaza daga doron kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce wannan ya saba doka kuma dukkan kasashe na da alhakin daukar mataki don kawo karshen halin da ake ciki.
Isra'ila ta yi kisan kare dangi a Gaza
Kwamitin ya ce Isra’ila ta aikata laifuffuka guda hudu daga cikin biyar da ake dangantawa da kisan kare dangi.
Wadannan sun hada da kashe mutane, haddasa musu mummunan lahani, takura wa musu da halin rayuwa da zai iya kawo halaka, da kuma hana haihuwa.
Rahoton ya kara da cewa manyan jami’an gwamnatin Isra’ila da na soja ne ke da alhakin aikata wadannan laifuffuka, bisa ga kalaman nuna kiyayya da suka yi a fili.
Tsananin halin rayuwa a zirin Gaza
Binciken ya gano cewa Isra’ila ta yi amfani da yunwa da takura wajen lalata rayuwar Falasɗinawa.
Bugu da kari, an rufe hanyar samun agaji, aka takaita abinci da ruwa, tare da kai hare-hare kan jama’a da suka haddasa mace-mace masu yawa.
Rahoton ya ce kusan mutum miliyan 1 ke zaune a Gaza cikin tsananin yunwa da hare-haren da suka wuce gona da iri, inda ake samun gazawa wajen samun abinci da kula da lafiya.
Isra'ila ta lalata cibiyoyin lafiya
Kwamitin ya kuma nuna cewa an ruguza gine-ginen kiwon lafiya da makarantu da gangan a hare haren Isra'ila a Gaza.
Rahoton ya ce Isra’ila ta yi watsi da umarnin kotun duniya (ICJ) da ta bukace ta ba da damar kai agaji cikin gaggawa ga Falasɗinawa a Gaza.
Pillay ta gargadi kasashen duniya cewa shiru kan wannan lamari zai zama amincewa da laifin da Isra'ila ke yi.

Source: Getty Images
BBC ta rahoto cewa Pillay ta ce doka ta tilasta wa kowace kasa daukar matakai da za su dakile kisan kare dangi da ake yi a Gaza.
Ta jaddada cewa rashin daukar mataki yanzu zai kara dagula al’amura tare da kara jefa al’ummar Falasɗinu cikin wani yanayi na tsanani da ba a taba gani ba.
Kasashen duniya sun goyi bayan Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa kasashen duniya guda 142 sun goyi bayan kafa kasar Falasdinawa a yankin Gaza.
Hakan na zuwa ne bayan kasashen sun kada kuri'a a karkashin majalisar dinkin duniya a makon da ya wuce.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce shi da Saudiyya ne suka jagoranci kira ga kasashe su goyi bayan Falasdinawa a kan Isra'ila.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


