Mutane Sun Mutu da Wani Karamin Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari, An Samu Bayanai

Mutane Sun Mutu da Wani Karamin Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari, An Samu Bayanai

  • Wani karamin jirgin sama ya gamu da hatsari a Yammacin kasar Jamus jim kadan bayan bacewarsa a ranar Lahadi
  • Hukumomin Jamus sun tabbatar da aukuwar lamarin a safiyar yau Litinin bayan gano falle-fallen jirgin tare da gawar mutanen da ke ciki
  • Mazauna yankin da abin ya faru sun nuna damuwa kan lamarin yayin da jami'an tsaro suka fara bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jamus - Mutum biyu sun mutu yayin da wani karamin jirgin sama ya yi hatsari a yammcin kasar Jamus da ke nahiyar Turai.

Rundunar ‘yan sanda a Jamus ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a hatsarin jirgin da ya auku a kusa da garin Bitburg, dab da iyakar ƙasar Luxembourg.

Hoton jirgi a sama.
Hoton wani jirgin sama yayin da yake tafiya sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar sanarwar ‘yan sanda, jirgin da ake kira ultralight aircraft ya ɓace tun daren Lahadi, lokacin da aka yi zaton zai sauka a filin jiragen sama na Bitburg, in ji rahoton People Gazettengr.

Kara karanta wannan

Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda karamin jirgin sama ya bata a Jamus

Rahoton ya nuna cewa a lokacin da aka rasa shi, an daina samun bayanai daga matuka jirgin, lamarin da ya haifar da damuwa ga hukumomin tsaro.

Sai dai da safiyar ranar Litinin, jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan kashe gobara suka gudanar da bincike a cikin yankunan karkara, inda daga bisani suka gano falle-fallen jirgin tare da gawarwakin mutane biyu da ke cikinsa.

Jaridar Artha Dabali ta ce an gano wurin da jirgin ya yi hatsarin ne a wani fili mai nisan kimanin kilomita shida daga Arewacin garin Bitburg.

Bincike kan musabbabin hatsarin jirgin

Hukumomin tsaro sun ce har yanzu ba a gano sunayen waɗanda suka mutu ba, saboda ana jiran tabbatar da su daga danginsu, sannan ba a tantance musabbabin hatsarin ba.

An bayyana cewa hukumar binciken hadurran jiragen sama ta Jamus ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa jirgin ya fado.

Kara karanta wannan

An nuna fuskar Kachalla Babaro da ya kai hari masallaci, ya kashe Musulmai

Bitburg, wanda ke da tazarar ƙasa da kilomita 30 daga iyakar Luxembourg, na ɗaya daga cikin ƙananan garuruwa masu muhimmanci a yammacin Jamus.

Filin saukar jiragen saman da hatsarin ya faru a kusa da shi, na yawan karɓar jirage ƙanana masu zaman kansu da na yawon shakatawa.

Hankulan mazauna yankin ya tashi

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru da dama da aka samu irin wannan hatsari a yankin.

Rahotanni sun ce lamarin ya tayar da hankalin al’ummar yankin, inda mazauna wurin suka nuna alhini da jimami kan aukuwar hatsarin.

Dakarun rundunar yan sandan Jamus.
Hoton jami'an yan sandan Jamus a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani mazaunin kauyen kusa da wurin da hatsarin ya faru ya shaida wa kafofin watsa labarai cewa sun ji ƙarar fashewa kafin su ga hayaki a saman jeji.

Hukumomi sun bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da bincike ke gudana.

Jirgin sojoji ya yi hadari a Venezuela

A wani rahoton, kun ji cewa wani ƙaramin jirgin sojin sama da ke ɗauke da 'yan wata ƙabilar Amazon ya fadi a dajin kasar Venezuela a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan daba: Masu shigar mata su yi kisan gilla sun bulla a Kano, an kama wasu

Ma’aikatar tsaron Venezuela ta ce mutum bakwai sun mutu, uku sun tsira daga haɗarin,, ciki har da matukin jirgin.

Binciken da hukumomin kasar suka gudanar ya nuna cewa haɗarin ya faru ne sanadiyyar matsalar na'ura da jirgin saman ya samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262