Watanni bayan Ya Rasu, An Gano Gidan da Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Mallaka a Landan

Watanni bayan Ya Rasu, An Gano Gidan da Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Mallaka a Landan

  • Kotun Landan ta yanke hukunci kan shari'a mai cike da rudani da aka shigar gabanta kan mallakar wani gida a Burtaniya
  • Bayan sauraron duka bangarorin da suka yi ikirarin mallakar gida, kotun ta gano cewa duka bayanan da suka gabatar karya ne
  • A karshe, an gano cewa gidan mallakin tsohon minista kuma tsohon gwamna a Najeriya, Marigayi Janar Jeremiah Useni ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

London, UK - An tafka rikicin shari'a a gaban kotun kadarori ta Landan da ke kasar Ingila kan mallakar wani gida da ke 79 Randall Avenue, London NW2.

Shari’ar ta taso ne bayan wata mai suna “Mis Tali Shani” ta kai ƙarar babban lauya a Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), tana cewa ita ce mai gidan da aka yi yunkurin canja sunan mallaka.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Jeremiah Useni.
Hoton marigayi tsohon ministan Abuja, Jeremiah Useni Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Tsohon gwamna ya mallaki gida a Landan

The Cable ta tattaro cewa, kotu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ewan Paton, ta yanke cewa duka mutanen biyu, “Ms Shani” da Ozekhome karya suke yi, babu wanda ya mallaki gidan daga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta tabbatar cewa asalin mai gidan shi ne marigayi Janar Jeremiah Useni, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon Gwamnan Jihar Bendel da aka rushe a shekarun 1980s da 1990s.

Useni, wanda ya rasu a Faransa a farkon wannan shekara, ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Yadda mutum 2 suka nemi kwace gidan

Shari’ar ta fara ne a 2023 lokacin da Ozekhome ya nemi a yi masa rajistar mallaka, yana cewa wani “Mr Tali Shani,” ne ya ba shi gidan kyauta saboda ayyukan lauya da ya taba yi masa.

Sai dai daga bisani wata “Mis Tali Shani” ta fito tana cewa ita ce mai gidan, abin da ya jefa shari’ar cikin ruɗani, inda maza da mata biyu masu suna iri ɗaya suka yi iƙirarin mallakar gida ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

Kotun ta gano abubuwa masu ban mamaki: takardun bogi, shaidar mutuwa da ta saba wa juna, batun yan uwantaka da babu hujja, da ma da’awar cewa hotunan jana’iza sun ɓace ne saboda 'yan bindiga sun kashe mai ɗaukar hoton.

Abubuwan da kotun na Landan ta gano

Bincike daga hukumar NIMC ya tabbatar da cewa lambar NIN da aka gabatar an yi ta ne ta hanyar zamba.

Har ila yau, bayanin “Mr Shani” cewa ya sayi gidan tun 1993 da kudin kiwo da mangwaro bai gamsar da kotu ba.

A ƙarshe, tsohon Janar Useni ya yi bayani a bidiyo kafin rasuwarsa, inda ya tabbatar cewa shi ne ya sayi gidan a 1993, amma ya yi rajista da sunan ƙarya “Philips Bincan” ko “Tali Shani”.

Hoton gidan da aka yi takaddama a kai a Landa n.
Hoton gidan da kotu ta tabbatar cewa na marigayi Janar Useni ne a Landan Hoto: GOADM
Source: Twitter

Kotu ta amince Janar Useni ne ya saya gidan

Kotun ta tabbatar da wannan da shaidun takardu na marigayi tsohon gwamnan. Alƙali Paton ya ce:

“Duka bangarorin biyu sun gaza. Ba ‘Mr’ ko ‘Ms Tali Shani’ suka mallaki gidan ba, hakikanin mai shi shi ne Janar Useni, wanda ya yi amfani da sunan ƙarya wajen rajista.”

A halin yanzu, kasancewar Useni ya rasu, kotu ta ce mallaka za ta koma ga duk wanda ya sami takardar gadon kadarorinsa a Ingila.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Matasan Arewa sun taso El Rufai a gaba, an ji dalili

An kama tsohon manajan NNPCL da laifi a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wata kotun tarayyar Amurka, ta samu tsohon babban manajan kamfanin NNPCL da laifin karɓar rashawar Dala miliyan 2.1.

Kotun ta gamau da cewa Paulinus Okoronkwo, wanda tsohon manaja ne a kamfanin NNPCL da aikata laifuffukan da suka haɗa da satar.kuɗi, karya dokar haraji da kuma kawo tsaiko a bincike.

Alƙalin kotun, John F. Walter, wanda ya jagoranci shari’ar, ya sanya 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar da zai yanke hukunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262